Jirgin kasa: Gwamatin tarayya ta soke jigilar fasinjoji kyauta da ta fara kafin zabe

Jirgin kasa: Gwamatin tarayya ta soke jigilar fasinjoji kyauta da ta fara kafin zabe

Babban ministan sufuri a tarayyar Najeriya kuma mamba na majalisar zartaswar gwamnatin Shugaba Buhari, Rotimi Amaechi ya ba 'yan Najeriya hakuri game da dakatar da jigilar fasinjoji a jirgin kasa kyauta da aka fara daga garin Iju zuwa Abeokuta gabanin zaben 2019.

Ministan na sufuri ya bayar da hakurin ne a yayin ziyarar dubiya da yake kaiwa a wata-wata a tashar jiragen kasar dake Ibadan da ke kula da zirga-zirga daga Legas zuwa Ibadan.

Jirgin kasa: Gwamatin tarayya ta soke jigilar fasinjoji kyauta da ta fara kafin zabe
Jirgin kasa: Gwamatin tarayya ta soke jigilar fasinjoji kyauta da ta fara kafin zabe
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sheikh Gumi yayi magana kan zabukan da za'a sake a Kano

Ya bayyana cewa kamfanin da yayi kwangilar aikin shimfida hanyar jirgin ne watau China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) ya dakatar da jigilar saboda dalilai na tsaron lafiya da dukiyoyin fasinjojin da ma'aikatan su.

Haka zalika ministan ya kuma bayyana cewa tuni sun yi magana da ma'aikatan kamfanin daga China kuma sun yi masa alkawarin zewa za su dawo ba da dadewa.

Daga karshe kuma Mista Amaechi dake zaman tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa yana da yakinin cewa ko da ba shi zai cigaba ba a matsayin ministan Sufuri to tabbas duk wanda zai dawo zai yi aiki tukuru domin karasa ayyukan da ya fara.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tun bayan hawan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, harkokin zirga zirgar jiragen kasa sun kara habaka a dukkan fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel