Kar ku kuskura ku murde zaben jihar Bauchi - PDP ta gargadi INEC

Kar ku kuskura ku murde zaben jihar Bauchi - PDP ta gargadi INEC

- Jam'iyyar PDP ta gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC akan soke zaben gwamna a jihar Bauchi

- Jihar Bauchi dai na daya daga cikin jihohin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zabensu a matsayin zaben da bai kammala ba

- PDP ta ce ta samu wasu takardun bayanin sirri daga ofishin INEC na jihar Bauchi, kan yadda za su murde zaben jihar, wanda ya ce zasu fallasa nan ba da jimawa ba

Jam'iyyar PDP ta gargadi shuwagabannin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu, akan yin wasa ko murde sakamakon zaben kananan hukumomi 14 na jihar da aka rigaya aka sanar na zaben gwamnan jihar.

Haka zalika PDP ta yi gargadin cewa idan har aka yi duba da irin yanayin da jihar ta ke ciki na yadda siyasar ta dau zafi da kuma yadda kan masu kad'a kuri'a ya waye, duk wani yunkuri na sauya sakamakon zaben, zai iya haddasa babbar matsala a jihar.

Jihar Bauchi dai na daya daga cikin jihohin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zabensu a matsayin zaben da bai kammala ba.

KARANTA WANNAN: Yadda rundunar 'yan sanda ta kashe Adikwu - Wanda ake zargi a fashin Offa

Kar ku kuskura ku soke zaben jihar Bauchi - PDP ta gargadi INEC
Kar ku kuskura ku soke zaben jihar Bauchi - PDP ta gargadi INEC
Asali: UGC

Sauran jihohin da hukumar ta tsaida ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta sake gudanar da zaben zagaye na biyu sun hada jihohin Benue, Sokoto, Adamawa, Kano da Filato.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP na kasa, Mr Kola Ologbondiyan, a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, ya bayyana cewa PDP na sane da wani shiri da wasu jami'an INEC ke yi na soke sakamakon zaben wasu kananan hukumomi da nufin kara yawan adadin kuri'un da aka soke daga 70,000 zuwa 184,555.

"Ganin cewa jam'iyyarmu ta PDP da dan takararmu, Sanata Bala Mohammed, su ne akan gaba da kuma jin kamshin nasara, ganin cewa Tafawa Balewa gidan PDP ne, wannan ne ya sa APC ta umurci INEC ta soke zaben wasu kananan hukumomin da nufin murde zaben da za a sake gudanarwa a ranar 23 ga watan Maris."

Ya ce PDP ta samu wasu takardun bayanin sirri daga ofishin INEC na jihar Bauchi, kan yadda za su murde zaben jihar, wanda ya ce zasu fallasa nan ba da jimawa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel