Yadda rundunar 'yan sanda ta kashe Adikwu - Wanda ake zargi a fashin Offa

Yadda rundunar 'yan sanda ta kashe Adikwu - Wanda ake zargi a fashin Offa

Daya daga cikin mutane biyar da ake kan tuhumarsu da gudanar da fashin bankin Offa, jihar Kwara a shekarar da ta gabata, Ayoade Akinnibosun, a ranar Juma'a ya shaidawa babbar kotun Ilorin cewa da gangan rundunar 'yan sanda ta kashe Michael Adikwu, daya daga cikin manyan wadanda ake zargi kuma wanda ya kitsa yadda fashin bankunan zai kasance, da ya jawo asarar rayuka da dama.

Da ya ke labarta yadda komai ya faru a gaban kotun a cikin wani yanayi na 'shari'a cikin shari'a', Ayoade ya kuma sanar da yadda rundunar 'yan sanda ta tilasta shi akan lallai sai ya alakanta fashin da suka kai da shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki.

Akinnibosun da wasu mutane biyu da ake kan tuhumarsu, Ibikunle Ogunleye da Adeola Abraham, sun yi ikirarin cewa rundunar 'yan sanda na tursasasu fadin abubuwan da basu faru ba da karfin tsiya.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: INEC ta yi Allah-wadai da rawar da sojoji suka taka a zaben Rivers

Yadda rundunar 'yan sanda ta kashe Adikwu - Wanda ake zargi a fashin Offa
Yadda rundunar 'yan sanda ta kashe Adikwu - Wanda ake zargi a fashin Offa
Asali: Depositphotos

Da ya ke amsa tambayoyi a wani zaman gwaji daga lauyan wanda ake karewa, Mathias Emeribe, Ayoade, wanda shi ne mutum na farko da ake zargi a fashin, ya yi ikirarin cewa wani Sifetan 'yan sanda mai suna Vincent da ke karkashin rundunar kwararru ta 'yan sanda (IRT) ne ya kashe Adikwu da gan-gan.

Shi kuwa Ogunleye ya ce: "Sun kawo marigayi Adikwu domin ya shafa mana kashin kaji, amma da mamakinsu sai ya ce bai ma taba ganinmu ba a rayuwarsa, wannan ne dalilin da ya sa Mr Vincent ya kashe shi nan take."

Alkalin da ke sauraron karar, mai shari'a Halimat Salman, ta dage shari'ar har sai ranar 25 ga watan Maris.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel