Da duminsa: INEC ta yi Allah-wadai da rawar da sojoji suka taka a zaben Rivers

Da duminsa: INEC ta yi Allah-wadai da rawar da sojoji suka taka a zaben Rivers

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana matakin da za ta dauka a nan gaba dangane da zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki a jihar Rivers, wanda ta dakatar a ranar 10 ga watan Maris, sakamakon rikici da aka tayar a mafiya yawan cibiyoyin tattara sakamakon zabe a jihar.

A ranar 15 ga watan Maris, hukumar zaben kasar ta gana da wani kwamiti da ta kafa domin tattara rahotanni kan zaben jihar Rivers da ta dakatar, inda a karshen zaman hukumar da kwamitin ne ta yanke shawarar daukar matakai kamar haka:

  • Cewar an gudanar da zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki a jihar a mafi yawan rumfunan zabe kuma an tattara sakamako tare da sanar da shi.,
  • Cewar akwai sakamakon zaben kananan hukumomi 17 daga cikin 21 kuma na adane a hannun hukumar zaben.
  • Cewar an tattara kuri'un mazabu 21 daga cikin 32 na majalisar dokokin jihar kafin hukumar INEC ta dakatar da zaben jihar
  • Cewar sojoji tare da wasu da ke dauke da muggan makamai sun tarwatsa cibiyoyin tattara sakamakon zabe na jihar da ya haddasa cin zarafi da cafke jami'an zabe ba bisa ka'ida ba, wanda kuma ya haddasa tsaikon tattara sakamakon zaben jihar

KARANTA WANNAN: Gishirin zaman duniya: Dalibai 13,000 sun yi rantsuwar fara karatu a jami'ar ABU

Haka zalike hukumar INEC ta yi Allah-wadai da irin muguwar rawar da sojoji suka taka a jihar Rivers na hargitsa tattara sakamakon zabe da kuma kokarin canja zabin al'ummar jihar.

Daga karshe hukumar ta bayyana ranar 20 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta sanar da matakinta kan yadda za ta gudanar da zabe a jihar Rivers domin kammala zaben rumfunan da ba a yi ba.

Bayanin haka, gaba daya yana kunshe a cikin wata sanarwa daga kwamishinan hukumar na kasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai da ilimantar da masu kad'a kuri'a, Festus Okye Esq, wacce aka rabawa manema labarai a ranar 15 ga watan Maris.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel