Arzikin Buhari ya ragu daga yadda ya ke a 2015 - Osinbajo

Arzikin Buhari ya ragu daga yadda ya ke a 2015 - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi tsokaci a kan arzikin Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Osinbajo ya gano cewar ya dara shugaban kasa arziki a lokacin da ya ga takardar bayyana kadarori na Buhari a 2015

- Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa a halin yanzu arzikin na Buhari ya ragu a kan abinda ya mallaka a 2015

A daren ranar Alhamis 14 ga watan Maris ne mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce akwai yiwuwar arzikin shugaban kasa Buhari ya ragu idan aka kwatanta da abinda ya mallaka a 2015.

The Nation ta ruwaito cewa mataimakin shugban kasar ya yi wannan furucin ne a wurin wata liyafar cin abinci da aka shirya a fadar Aso Villa domin karrama wadanda suka taimaka wa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) neman kuri'u lokacin yakin neman zaben 2019.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

Ya ce: "Na duba takardan bayyana kadarori na shugaban kasa a shekarar 2015 inda na gano na fi shi arziki kuma na ce masa, "Shugaban kasa, Na fi ka arziki sosai, wannan abin kunya ne."

"Sai ya amsa da cewa, "Ni fa soja ne, kai kuma babban lauya ne saboda haka ya dace ka fi ni arziki."

"Maganan gaskiya shine arzikinsa sun ragu a kan yadda na gani a 2015 a yayin da na sake ganin takardan bayyana kadarorinsa."

A yayin da ya ke tsokaci a kan zabukan da za a maimaita a wasu jihohi shida a ranar 23 ga watan Maris, Osinbajo ya bukaci 'yan Najeriya su zabi jam'iyyar APC.

"Har yanzu ba mu kammala zabe ba.

"A ranar 23 ga watan Maris akwai zaben da za muyi a wasu jihohi shida kuma muna da 'yan takara.

"Ba zai yiwa mu yi nade hannu mu ce mun gama aiki ba, har yanzu akwai sauran aiki," inji Osinbajo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel