Rochas Okorocha ya mutu murus a siyasa - Jigo a APC

Rochas Okorocha ya mutu murus a siyasa - Jigo a APC

Dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Hope Uzodinma ya ce Gwamna Rochas Okorocha ya mutu murus a siyasance.

Ya ce abinda ya dace shine gwamnan ya nemi gafara a wurin al'ummar jihar bisa mulkin rashin adalci da ya yi musu a maimakon neman wadanda zai dora wa laifin da ya aikata.

A sakon da ya fitar a Abuja, Uzodinma ya ce ya kamata Okorocha ya mutunta kansa ya koma gefe guda a maimakon yi masa sharri da shugban jam'iyya na kasa biza gazawarsa na dora surukinsa a kan kujerar mulki a jihar.

Rochas Okorocha ya mutu murus a siyasa - Jigo a APC
Rochas Okorocha ya mutu murus a siyasa - Jigo a APC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

A yayin da ya ke mayar da martani a kan kalaman da Okorocha ya yi na cewa APC ta gaza lashe zabe a jihar saboda tsayar da Uzodinma ne, ya tunatar da gwamnan cewa shi kansa ya gaza kawo akwatinsa a zaben sanata duk da cewa shine gwamna mai ci a yanzu hakan yasa ya tilastawa baturen zabe sanar da cewa shine ya lashe zabe.

"Tunani shine ya kamata Okorocha ya boye fuskansa saboda kunya bayan ya yi rashin nasarar dora surukinsa a matsayin gwamnan jihar Imo kuma ya gaza lashe zaben sanata.

"Duk da biliyoyin naira da ya kashe domin ganin na fadi zabe a jihar, na lashe zaben kuma zamu gabatar da hujjan hakan.

"Amma Okorocha ya rasa kimarsa a siyasa kuma ya mutu murus a siyasance. Ya kware wurin karya al'umma amma yanzu Allah ya yi maganinsa.

"Ina tsamanin a yanzu ya dace ya rika neman afuwar mutanen jihar Imo saboda laifukan da ya yi musu da laifukan da ya yiwa Allah.

"Zan kwato nasara ta da Okorocha da Ihedioha suka kwace a makon da ta gabata sannan sannan zan samu abin fadawa Okorocha," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel