Dakarun soji sun yiwa wasu ‘yan fashi raga-raga a karamar hukumar Guma, hotuna

Dakarun soji sun yiwa wasu ‘yan fashi raga-raga a karamar hukumar Guma, hotuna

Dakarun sojojin Najeriya na runduna ta musamman na mai lamba 72 da ke garin Yelwata a karamar hukumar Guma da ke kan iyakar Benue da Nasarawa sun ce sunyi arangama da ‘yan fashi da makami hanyar Yelwata zuwa Kadarko yayin da suke sintiri a safiyar ranar 15 ga watan Maris na 2019.

‘Yan fashi da makamin suna sanye da kayan sojoji ne kuma suna yiwa mutane fashi a hanyar.

Sai dai jaruman sojojin sunyi nasarar fatatakan ‘yan fashin inda har suka yi nasarar kashe guda daga cikinsu yayinda sauran suka tsere.

Sojojin kuma sunyi nasarar kwato makamai da suka hada da bindigu da alburusai daga hannun yan fashin.

Ga hotunan wanda aka kashe da makaman da ka samu daga hannunsu.

Dakarun soji sun yiwa wasu ‘yan fashi raga-raga a karamar hukumar Guma, hotuna
Gawar dan fashi sanye da kayan sojoji da dakarun sojin Najeriya suka kashe a karamar hukumar Guma
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

Dakarun soji sun yiwa wasu ‘yan fashi raga-raga a karamar hukumar Guma, hotuna
Kwayoyi da sojojin Najeriya suka kwato daga wurin 'yan fashi da makami
Asali: Twitter

Dakarun soji sun yiwa wasu ‘yan fashi raga-raga a karamar hukumar Guma, hotuna
Alburussai da dakarun sojojin Najeriya suka kwao daga hannun yan fashi da makami a kan iyar Benue da Nasarawa
Asali: Twitter

Dakarun soji sun yiwa wasu ‘yan fashi raga-raga a karamar hukumar Guma, hotuna
'Yan fashi da makami da dakarun sojojin Najeriya suka kama a karamar hukumar Guma
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel