'Yan ta'addan IS sun dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a jihar Borno

'Yan ta'addan IS sun dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a jihar Borno

Kungiyar ta'addacin nan ta IS dake da hedikwatar ta a gabas ta tsakiya, ta ce ita ce ta kitsa, ta shirya sannan kuma ta aiwatar da kai wa wasu jami'an rundunar sojojin Najeriya hari a jihar Borno dake a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kungiyar IS ta fitar inda ta ce dan kunar bakin waken a cikin wata mota ne ya kai hari a wani gungun sojoji a garin Arege kusa da tafkin Chadi.

'Yan ta'addan IS sun dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a jihar Borno
'Yan ta'addan IS sun dauki alhakin kai harin kunar bakin wake a jihar Borno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari zai siyar da wasu kadarorin gwamnati - Shehu Sani

Harin na kunar bakin wake dai ba a saba ganin kungiyar na kai irinsa ba, ganin ta fi amfani da bindigogi ko kuma abubuwan fashewa wajen kai wa rundunar sojin Najeriya hari.

Amma a nasu bangaren, rundunar sojin ta Najeriya da take mayar da martani akan sanarwar ta kungiyar IS, ta ce dakarun hadin gwiwar ta da sauran kasashen dake makwaftaka da tafkin Chadi sun fafata da mayakan kungiyar, kuma sun kashe 'yan bindigar 33 tare da kwace makamai da motoci.

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da aiki da rundunonin kasa da na sama daga Kamaru da Nijar don yaki da masu tayar da kayar bayan.

A watan jiya ne kungiyar masu ikirarin jihadi suka kai hare-hare a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, a wani tunkuri na tarwatsa zabukan da aka gudanar a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel