Waiwaye: Dukkan Sanatocin da suka bar APC a 2018 sun fadi zabe sabanin mutum daya (Kalli jerinsu)

Waiwaye: Dukkan Sanatocin da suka bar APC a 2018 sun fadi zabe sabanin mutum daya (Kalli jerinsu)

Hausawa sukace waiwaye adon tafiya. Legit.ng Hausa ta yi muku waiwaye kan abubuwan da suka faru a majalisar dattawan Najeriya a shekarar 2019.

Za ku tuna cewa dare daya sanatoci akalla 15 suka sauya sheka daga jam'iyyar All Progressive congress zuwa jam'iyyar Peoples Democratic PDP, Peoples Redemption Party PRP da AfricanDemocratic Party ADC.

Legit.ng ta lura cewa bisa ga jerin sunayen zakarun zaben majalisaar dattawa da hukumar INEC ta saki, mutum daya kacal cikin wadannan sanatoci zai kara lomar taliya a majalisar. Sanata Dino Melaye ne kacal ya samu tikitin dawowa yayinda sukkan abokansa sun fadi a zabe, ko kuma basu sake takara ba.

Ga jerinsu:

Sanatocin da suka bar APC

1. Dino Melaye (Kogi ta yamma)

2. Barnabas Gemade (Benue ta gabashin arewa)

3. Ibrahim Danbaba (Sokoto ta kudu)

4. Shaaba Lafiaji (Kwara ta arewa)

5. Mohammed Shitu (Jigawa ta yamma)

6. Rafiu Ibrahim (Kwara ta kudu)

7. Suleiman Hunkuyi (Kaduna ta arewa)

8. Isa Misau (Bauchi ta tsakiya)

9. Monsurat Sunmonu (Oyo ta tsakiya)

10. Usman Nafada (Gombe ta arewa)

11. Musa Kwankwaso (Kano ta tsakiya)

12. Suleiman Nazif (Bauchi ta arewa)

13. Abdul-Aziz Murtala Nyako (Adamawa ta tsakiya)

14. Shehu Sani (Kaduna ta tsakiya)

15. Bukola Saraki (Kwara ta tsakiya)

KU KARANTA: Waiwaye: Dukkan yan majalisan wakilan da suka bar APC a 2018 sun fadi zabe sabanin mutune 2

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel