Buhari ba zai saka baki a zaben shugaban majalisar dattawa ba - Fadar shugaban kasa

Buhari ba zai saka baki a zaben shugaban majalisar dattawa ba - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa duk wanda ke da ra'ayin takara wani matsayi a shugabancin majalisar dattawa da majalisar wakilai ya san cewa shugaba Buhari ba zai taimakesa ba.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin babban hadimin shugaban kasa kan alakar fadar da majalisa, Ita Enang, inda yake jawabi ga manema labarai a zauren majalisar dokokin tarayya ranar Juma'a, 15 ga watan Maris, 2019.

Game da cewarsa, shugaban kasa mutum ne wanda yayi imani da doka, saboda haka zai bar dukkan bangarorin gwamnati suyi ayyukansu kamar yadda kunin tsarin mulkin kasa ya tanada ba tare yi musu shisshigi ba.

Yace: "Ka'idar shugaba Muhammadu Buhari shine dukkan bangarorin gwamnati suyi aikinsu bsa kundin tsarin mulki. Shi (Buhari) ba zai ketare iyakar da kundin tsarin mulki tayi masa ba."

Za ku tuna cewa wasu sabbin sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress ( APC ) a rranar Alhamis bayan karbar takardar shaidar nasara a zabe sun bayyana cewa fadar shugaban kasa da uwar jam'iyya suyi gaggawan bayyana musu wanda zasu zaba matsayin shugabannin majalisar.

Sabbin yan majalisan sun yi wannan magana ne kan irin rikici da sabanin da aka samu a shekarar 2015 inda Bukola Saraki ya hada baki da jam'iyyar adawa wajen zaben shugabannin majalisar dattawa.

KU KARANTA: Daga karshe, APC ta cira tsintsiyar karfen da aka dasa a kofar shiga birnin Abuja

Kana sun gargadi shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin jam'iyyar APC da su zaba musu wadanda suka cancanta saboda gudun kada abinda ya faru a baya ya maimaita kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel