Sheikh Gumi yayi magana kan zabukan da za'a sakeyi a Kano, Sokoto, Adamawa da Bauchi

Sheikh Gumi yayi magana kan zabukan da za'a sakeyi a Kano, Sokoto, Adamawa da Bauchi

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake zaune a garin Kaduna, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yayi kira ga dukkan daukacin mutanen jahohin nan da za'a sake zaben gwamna musamman ma wadanda ke da rinjayen musulmi da su zauna lafiya.

Malamin dai yayi wannan kiran ne a ranar Alhamis din da ta gabata a karshen karatun sa da yake yi na littafin Akidatus Sahiha a masallacin Sultan Bello, garin Kaduna.

Sheikh Gumi yayi magana kan zabukan da za'a sakeyi a Kano, Sokoto, Adamawa da Bauchi
Sheikh Gumi yayi magana kan zabukan da za'a sakeyi a Kano, Sokoto, Adamawa da Bauchi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matasa sun jefi gwamnan Legas da duwatsu

Haka ma dai malamin ya yi kira ga mutanen jahohin da za'a sake zaben kamar Kano, Sokoto, Adamawa da Bauchi musamman ma a garuruwan da aka tsara yin zaben da su fito cikin lumana su zabi wanda suke so da zai taimakawa addini.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan gari a unguwar Itafaji dake a garin Legas mun samu labarin cewa sun yiwa gwamnan jihar Akinwunmi Ambode ruwan duwatsu yayin da yake barin wurin ginin makarantar nan da ya ruguje da daliban Firamare akalla 80.

Su dai mutanen garin wadanda ke cikin yanayi irin na kaduwa da bakin ciki, sun tattaru a wurin makarantar suna alhini tare da ayyukan ceto sauran yaran da ake tunanin buraguzan gini ya danne su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel