Yanzu-yanzu: Bayan Legas, wani gini ya kara rushewa a Ibadan

Yanzu-yanzu: Bayan Legas, wani gini ya kara rushewa a Ibadan

Rahoton da muka samu daga Sahara Reporters na cewa wani gini ya sake rubzo wa mutane a unguwar Bode da ke garin Ibadan na jihar Oyo a yau Juma'a 15 ga watan Maris na 2019.

Lamarin ya faru ne a unguwar Bode bayan gadar Molete a garin Ibadan.

Wannan na zuwa ne sa'o'i 72 bayan wani bene ya rubzo wa al'umma ciki har da 'yan makaranta a unguwar Ita Faji na jihar Legas.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

Yanzu-yanzu: Wani gini ya sake rubuzo wa al'umma a Ibadan
Yanzu-yanzu: Wani gini ya sake rubuzo wa al'umma a Ibadan
Asali: UGC

A halin yanzu ba a san adadin mutanen da ginin ya rubzo wa ba ko adadin wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata sai dai al'umma da dama sun taro a wurin da ginin ya rushe.

Majiyar Legit.ng ta gano cewar har yanzu masu ceto wadanda ginin ya rubzo musu basu da yawa, hakan na nufin rayuwar al'umma da dama yana cikin hadari.

Ku cigaba da kasancewa tare da mu domin karin bayani...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel