Buhari zai sayar da wasu manyan kadarorin gwamnati, ya saka kudin a kasafin kudin 2019

Buhari zai sayar da wasu manyan kadarorin gwamnati, ya saka kudin a kasafin kudin 2019

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kudurta sayar da wasu manyan kadarorin gwamnatin ta tarayya a shekarar nan ta 2019 domin saka kudin a kasafin kudin shekarar, inji Sanata Shehu Sani.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wani sakon da fitaccen Sanatan ya wallafa a shafin sa na dandalin sadarwar zamni na Tuwita ranar Alhamis din da ta gabata.

Buhari zai sayar da wasu manyan kadarorin gwamnati, ya saka kudin a kasafin kudin 2019
Buhari zai sayar da wasu manyan kadarorin gwamnati, ya saka kudin a kasafin kudin 2019
Asali: Twitter

KU KARANTA: An tsinci gawar dan kasar wajen da aka sace a Kano

Sanatan dan jam'iyyar PRP wanda ya rasa kujerar sa a zaben da aka gudanar ya ce bai san ko yaya gwamnatin ta APC zata yi ba wajen gamsar da 'yan Najeriya har su rungumi siyar da kadarorin gwamnatin musamman yadda su da kan su suka soki hakan a lokacin gangamin yakin neman zaben da ya gudana.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jam'iyyar ta APC ta yi ta sukar kudurin siyar da rukunin kamfanonin NNPC da dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai yi idan ya lashe zabe a baya.

Yanzu dai kam abun lura a tsaya a gani shine kadarorin da za'a saida kuma suwa za su siye su da kuma irin ra'ayoyin talakawan kasar akan hakan.

Ga dai abun da Sanatan ya wallafa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel