Yan sanda na so na shafa ma Saraki kashin kaza – Wani da ake zargi da hannu a fashin Offa

Yan sanda na so na shafa ma Saraki kashin kaza – Wani da ake zargi da hannu a fashin Offa

Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a fashin Offa, karamar hukumar Offa, jihar Kwara wanda aka yi a ranar 5 ga watan Afrilu 2018, Ayoade Akinnibosun aa ranar Juma’a, 15 ga watan Maris yace yan sanda sun nemi ya shafa wa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kashin kaza, jaridar The Nation ta ruwaito.

Akinnibosun tare da wasu mutum biyu, Ibikunle Ogunleye (wanda ake zargi na biyu) da kuma Adeola Abraham (wanda ake zargi na uku) sun bayar da bayanin yadda yan sanda ke karban jawabai daga gare su ta karfin tuwa a wata babbar kotun jihar Kwara, da ke Ilorin.

Sauran wadanda ake zargi Salaudeen Azeez da Niyi Ogundiran na a kotu.

Yan sanda na so na shafa ma Saraki kashin kaza – Wani da ake zargi da hannu a fashin Offa
Yan sanda na so na shafa ma Saraki kashin kaza – Wani da ake zargi da hannu a fashin Offa
Asali: Facebook

Mutanen da ake zargi su uku sun kuma bayyana cewa wani Inspekta Vincent ne ya harbe babban wanda ake zargi a harin Michael Adikwu har lahira.

KU KARANTA KUMA: Sai na kwato yanci na da aka sace a Zamfara — Dan takaran jam’iyyar PDP

An rahoto cewa rundunar yan sanda ta sanar da cewa Adikwu ya fadi ne a inda yake tsare sannan aka yi gaggawan kai shi asibiti kafin ya mutu.

Mai shari’a, Justis Halimat Salman ta dage sauraron karan zuwa ranar 25 ga watan Maris don ci gaba da shari’an.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa matsalar tsaro ta tilasta alkalin babbar kotun jihar Kwara da ke da zama a Ilorin dage sauraron shari'ar mutane biyar da ake zarginsu da gudanar da fashi da makami a wani banki da ke Offa, jihar Kwara.

Wannan ya faru ne bayan da kotun ta fara sauraron karar da aka shigar, inda aka gabatar mata da wani da lamarin ya auku a gabansa, Hitila Hassan, karkashin jagorancin jami'i mai shigar da kara, Wahab Egbewole, kuma ya samu tantancewa daga lauyan wadanda ake kara, Mathias Emeribe.

Alkalin da ke sauraron karar, mai shari'a Halimat Salman, wacce ta dage sauraron karar, ta ce ta yanke hukuncin daukar matakin ne saboda kiyaye lafiya da rayukan kowa da ke cikin kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel