'Yan takarar gwamna 20 sun goyi bayan maimaita zabe a Bauchi

'Yan takarar gwamna 20 sun goyi bayan maimaita zabe a Bauchi

Hadakar yan takarar gwamna 20 a jihar Bauchi sun amince da matakin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC tayi na sake maimaita zabe a jihar.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa baturen zabe na jihar, Dr Mohammed Kyari ya sanar da cewa zaben ba ta kammala ba saboda an samu matsaloli yayin zaben a karamar hukumar Tafawa Balewa da wasu rumfunan zabe a jihar.

Baturen zaben kuma ya sanar da cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu kuri'u 102,000 inda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri'u 56,000 a karamar hukumar Bauchi.

DUBA WANNAN: Zargin sayen kuri'a: Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin fitar da miliyan 233

'Yan takarar gwamna 20 sun goyi bayan maimaita zabe a Bauchi
'Yan takarar gwamna 20 sun goyi bayan maimaita zabe a Bauchi
Asali: UGC

A yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Bauchi, Mai magana da yawun 'yan takarar kujerar gwamnan, Alhaji Bello Abubakar ya bukaci INEC ta sake gudanar da zaben a akwatunnan zaben da lamarin ya shafa.

"Tunda hukumar zaben ta ce za ta sake gudanar da zabe a wasu wurare, muna goyon bayan ayi hakan saboda cigaban al'ummar jihar Bauchi.

"Yan takarar kujerar gwamnan sun fito ne daga jam'iyyun ADC, PDC, DA, AD, MPN, DPC, NEPP, MMN, SDP and KOWA.

"Sauran sun hada da ACDN, PPN, BNPP, APP, NRM, UPN, SNP, APA, AA and AGA,” inji shi.

A bangarensa, dan takarar gwamna na jam'iyyar Nigeria Element Professional Party (NEPP), ya yabawa INEC a kan matakin da ta dauka ya kuma shawarci al'umma su kwantar da hankulansu.

"Muna kira ga al'umma su zauna lafiya yayin zaben da bayan zaben da za a gudanar a ranar 23 ga watan Maris na 2019.

"Kada ku bari kowa ya yi amfani da ku wurin tayar da fitina musamman wadanda ba su kaunar jihar mu. Ina tunanin dukkan mu muna son cigabar jihar mu," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel