Sai na kwato yanci na da aka sace a Zamfara — Dan takaran jam’iyyar PDP

Sai na kwato yanci na da aka sace a Zamfara — Dan takaran jam’iyyar PDP

Dan takaran gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 9 ga watan Maris a Jihar Zamfara, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana cewa zai kwato yancin shi da aka sace a rubutacciyar kara da ya gabatar a kotu.

Dr. Matawalle, wanda ya sha kaye a hannun dan takaran APC, Hon. Muktar Idris, bisaga sakamokon zabe da hukumar INEC ta bayyana, ya fada wa manema labarai a ranar juma’a a Abuja, cewa yana da tabbacin cewa hukuncin da kotun za ta yanke zai kyautata masa tunda ya kasance da takardun shaida akan zaben.

Sai na kwato yanci na da aka sace a Zamfara — Dan takaran jam’iyyar PDP
Sai na kwato yanci na da aka sace a Zamfara — Dan takaran jam’iyyar PDP
Asali: Facebook

“Duk da cewar hukumar INEC ta yi zargin cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar sannan jam’iyyar APC a Zamfara ba za ta kasance cikin zaben 2019 ba, gwamnan Abdulazeez Yari yayi barazanar hana gudanar da zabe a jihar idan ba a saka APC ba a zaben.

“Gwamnatin Tarayya ta baiwa gwamnan goyon baya ta hannun ministan shari’a wanda ya kaddamar da daukakkiyar hukunci wacce ta shafe hukuncin babban kotun.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 14 na majalisar dokokin jahar Nassarawa

“Kwana biyu kafin zaben, hukumar INEC ta ce, a karkashin umurnin kotu, jam’iyyar APC a Zamfara zata halarci zaben. Zaben gwamna da na yan majalisan sun kasance da magudi da razana.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel