Babu wani shugaban da aka taba yi a Najeriya dake amincewa da dokoki kamar Buhari

Babu wani shugaban da aka taba yi a Najeriya dake amincewa da dokoki kamar Buhari

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkar majalisar dattawa, Sanata Ita Enang ya bayyana cewa babu wani shugaban kasa da aka taba yi tun 1999 daya amince da kafa sabbin dokoki kamar Buhari.

Legit.ng ta ruwaito Enang ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake musanta zargin da ake yi ma Buhari na kasancewa shugaban da yafi watsi da dokokin da majalisar ta yi tare da kin rattafa hannu akansu.

KU KARANTA: INEC ta mika ma hadiman Buhari su 2 shaidar lashe zaben yan majalisar wakilai

Babu wani shugaban da aka taba yi a Najeriya dake amincewa da dokoki kamar Buhari
Buhari da Enang
Asali: UGC

“Babu shakka babu wata majalisa a tarihin Najeriya tun daga 1999 data samar da dokoki kamar majalisa ta 8, amma ba gaskiya bane ace Buhari baya amincewa da dokokin, domin kuwa babu wani shugaban daya kaishi sa hannu akan dokoki tun daga 1999, don haka ya cancanci yabo.

“Amma a duk lokacin da shugaban kasa yaki rattafa hannu akan doka tare da yin watsi da ita, tabbas yayi haka ne saboda mafificin amfanin yan Najeriya ne, kuma dokar na tattare da matsaloli, yan kasa ne ya kamata su kai bangaren zartarwa da bangaren dokoki gaban kotu don jin dalili.

“Na sani idan Buhari yayi fatali da dokar da majalisa tayi, tabbas dayan biyu ne, kodai dokar ta ci karo da kundin tsarin mulki, ko kuma ta ci karo da dokokin dake akwai, a wasu lokutan kuma dokokin zasu janyo asarar kudaden shiga ga gwamnati.” Inji shi.

Enang ya bada misalin dokar kafa hukumar kula da albarkatun man fetir, PRC, da majalisa tayi, amma Buhari yayi watsi da ita sakamakon dokar ta nemi a bada makudan kudi ga hukumar, ta yadda ba za’a samu isashshen kudin rabama gwamnatocin jahohi, tarayya da na kananan hukumomi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel