Aisha Buhari ta mika ta’aziyyar ta ga iyalen wadanda rushewar gini ya cika da su a Legas

Aisha Buhari ta mika ta’aziyyar ta ga iyalen wadanda rushewar gini ya cika da su a Legas

- Aisha Buhari ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasa ransu a sanadiyan rushewar gini a Legas

- An ruwaito labarinmutuwar wasu yara sanadiyar rushewar gini da ya afku a yankin Faaji da ke Lagas a ranar Laraba, 13 ga watan Maris

- Uwar gidar Buhari tace tayi bakin ciki matuka da mutuwar kananan yara da basu san komai ba yayinda tayi addu’an Allah ya ba iyalansu juriyar wannan rashi nasu

Uwar gidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta mika ta’aziyyar ta ga iyalen wadanda suka rasa rayukan su a sanadiyan rushewar gini a yankin Itafaji da ke jihar Legas.

Aisha, a sakon ta’aziyya da ta aika ta shafin ta na twitter a ranar juma’a, 15 ga watan Maris ta roki Allah da ya kara wa wadanda suka yi rashi hakuri.

A halin da ake ciki mun ji cewa bayan rushewar da ginin wani makaranta da ke unguwar Faji na jihar Legas ya yi a jiya, Gwamna Akinwunmbi Ambide na jihar ya dau alwashin rushe dukan gine-ginen makarantun da akayi ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA KUMA: An haifi jaririya dauke da rubutun sunan Allah a Sokoto

Channels TV ta ruwaito cewa Ambode ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba 13 ga watan Maris yayin da ya ke mayar da martani a kan damuwar da wasu mazauna unguwar suka nuna a kan makarantun da aka gina ba bisa ka'ida ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel