INEC ta mika ma hadiman Buhari su 2 shaidar lashe zaben yan majalisar wakilai

INEC ta mika ma hadiman Buhari su 2 shaidar lashe zaben yan majalisar wakilai

A ranar Alhamis, 14 ga watan Maris ne hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta gudanar da taron mika shahadar cin zabe ga yan takarkarun majalisar dattawa dana majalisar wakilai da suka samu nasara a zabukan data gudanar makonni uku da suka shude.

Legit.com ta ruwaito daga cikin wadanda suka amshi wannan shahada daga hukumar INEC akwai wasu hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari guda biyu, da suka hada da Abdulrahman Kawu Sumaila da Sha’aban Ibrahim Sharada, dukkaninsu yan asalin jahar Kano.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe Musulmai 40 yayin da suke sallar Juma’a a Masallatai 2

INEC ta mika ma hadiman Buhari su 2 shaidar lashe zaben yan majalisar wakilai
Buhari da Kawu
Asali: Facebook

Shi dai Kawu Sumaila ya kasance kafin wannan nasarar da yayi, shine mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar majalisar wakilai, yayin da Sha’aban Sharada ke rike da mukamin hadimin shugaban kasa akan harkar watsa labaru ta rediyo.

Sai dai yayin da Sharada ya lashe zaben wakiltar mazabar kwaryar cikin birnin Kano a majalisar wakilai, shi kuwa Kawu Sumaila ya lashe zaben wakiltar mazabar Sumaila da Takai ne, mukamin daya taba rikewa a baya, har karo uku. Dukkaninsu yan jam’iyyar APC ne.

INEC ta mika ma hadiman Buhari su 2 shaidar lashe zaben yan majalisar wakilai
Buhari da Sha'ban
Asali: Facebook

Ana sa ran rantsar da yan majalisar bayan an rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, kuma jam’iyyar APC ce keda yan mafi rinjaye a a majalisar wakilai, inda take da yan majalisu guda 211 cikin yan majalisu 360 da majalisar ta kunsa.

A wani labarin kuma, hukumar INEC ta hana tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha shaidar lashe zaben Sanatan mazabar Orlu ta jahar Imo da ya tsaya takara, kuma yake ikirarin lashe zaben, inda tace ta dauki wannan mataki ne sakamakon Rochas ya tilasta ma baturen zabe ya sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, a yanzu dai INEC na nazarin matakin da zata dauka akansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel