Yanzu yanzu: An saki surukar Gwamna Masari da aka yi garkuwa da ita

Yanzu yanzu: An saki surukar Gwamna Masari da aka yi garkuwa da ita

- Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun saki surukar Gwamna Masari da suka yi garkuwa da ita

- An sako ta cikin koshin lafiya sannan kuma a halin yanzu ta koma ga yan uwanta bayan gwaje gwaje da aka kammala

Surukar Gwamna Aminu Masari, Hajiya Hauwa Yusuf ta dawo gida bayan wadanda suka sace ta sun sako ta bayan shafe kwanaki 8 da ta yi a hannun su.

Kakakin rundunan yan sanda reshen Katsina, SP Gambo Isah yace an sako ta cikin koshin lafiya sannan kuma a halin yanzu ta koma ga yan uwanta bayan gwaje gwaje da aka kammala.

Yanzu yanzu: An saki surukar Gwamna Masari da aka yi garkuwa da ita
Yanzu yanzu: An saki surukar Gwamna Masari da aka yi garkuwa da ita
Asali: Twitter

Ku tuna a baya cewa rundunan yan sanda tace suna bin duddugin wani wanda ake zargin yana da hannu cikin lamarin.

Anyi garkuwa da Hajiya Yusuf ne a Gidan ta dake a Dundume Crescent a Katsina, a ranar juma’a da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Zaben Nasarawa: Dan takarar gwamna a PDP ya ki amincewa da sakamakon zabe, ya doshi kotu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar matar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

Legit.ng ta tattaro cewa yan bindigan sun kai farmaki gidan dattijuwar surukar gwamnan da ke Katsina akan Babura sannan suka tafi da ita.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel