Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da sake kwace N2.4bn da ke da nasaba Patience Jonathan

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da sake kwace N2.4bn da ke da nasaba Patience Jonathan

- A ranar juma'a ne kotun koli ta Najeriya ta tabbatar da kwace kudi Naira biliyan 2.4 na wucin gadi

- Kotun ta gano kudin yana da dangantaka da uwar gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Bai wuce mako daya daya ba da aka kwace wasu dala miliyan 8.4 daga wani kamfani da ake zargin yana da dangantaka da Patience Jonathan

A ranar juma'a ne kotun koli ta tabbatar da kwacen wucin gadi da babbar kotun jihar Legas tayi na kudi Naira biliyan 2.4 wanda ake zargin mallakin matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misis Patience Jonathan.

Bai wuce sati daya ba kenan da kotun kolin ta tabbatar da kwace dala miliyan 8.4 wanda mallakin tsohuwar uwar gidan shugaban kasan ne tare da umartar ta da ta bayyana gaban babbar kotun jihar Legas din don bayyana dalilan da zasu hana gwamnatin tarayya mallake kudin na ang dindindin.

A ranar juma'ar ne a shari'a mabambanciya kotun ta gurfanar da wasu mutane biyar da suka danganci kudi Naira 2,421,953,522 mallakin Lawari Furniture & Bath Limited, kamfanin da hukumar yaki da rashawa ta gano yana da hadi da matar Jonathan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: An saki surukar Gwamna Masari da aka yi garkuwa da ita

Lawari Furniture & Bath Limited, ta hannun lauyan ta, Chief Mike Ozekhome (babban lauyan Najeriya), ya daukaka kara don kalubalanta hukuncin ranar 12 ga watan janairu, 2018 a kotun daukaka kara ta jihar Legas. Inda a nan ne aka tabbatar da kwace Naira biliyan 2.4 na wucin gadi wanda umarnin babban kotun tarayya ce ta Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel