An haifi jaririya dauke da rubutun sunan Allah a Sokoto

An haifi jaririya dauke da rubutun sunan Allah a Sokoto

Rahotanni da ke zuwa mana yayi ikirarin cewa an haifi wata jaririya dauke da rubutun sunan Allah a wasu bangarori na jikinta ciki harda kirjinta. Anyi zargin cewa yarinyar na dauke da rubutune a jirginta, jinta da kuma bayanta.

An tattaro cewa an haifi jinjirar ne a ranar 2 ga watan Maris, sannan kuma haihuwarta ya janyo hankulan mazauna Sokoto da dama wadanda ke tururuwan zuwa ganin abunda mahaifiyar yarinyar, Saratu Yusuf ta bayyana a matsayin baiwa daga Allah.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an haifi yarinyar a cikin iyalai hudu. An kuma haife ta ne a asibitin yan sanda da ke hanyar Barth Sokoto, mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa ta haifeta kamar kowa sannan cewa ba ta fuskanci wani bakon lamari ba a lokacin da take dauke da cikin yarinyar.

An haifi jaririya dauke da rubutun sunan Allah a Sokoto
An haifi jaririya dauke da rubutun sunan Allah a Sokoto
Asali: UGC

Saratu wacce ta haifi jinjirar tare da mijinta na shekara 16, Alhaji Hussaini, ta bayyana cewa ta lura da yadda fatar jikin yarinyar yaki huduwa. Ta bayyana cewa a lokacin da suka yi kokarin huda mata kunne, ba abunda ya shia jikinta.

KU KARANTA KUMA: Zaben Nasarawa: Dan takarar gwamna a PDP ya ki amincewa da sakamakon zabe, ya doshi kotu

Da take nuna farin cikinta, mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa abun farin ciki ne samun irin wannan baiwar a gidanta. Ta kuma bayyana cewa yarinyar ta janyo hankulan baki daga kananan hukumomi daban-daban na Sokoto sannan cewa ta koma wani wuri mai shiru saboda hayaniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel