Gishirin zaman duniya: Dalibai 13,000 sun yi rantsuwar fara karatu a jami'ar ABU

Gishirin zaman duniya: Dalibai 13,000 sun yi rantsuwar fara karatu a jami'ar ABU

- Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria ta rantsar da dalibai 13,000 bayan samun gurbin karatunsu a zangon shekarar 2018/2019

- Shugaban jami'ar, Farfesa Ibrahim Garba ya bukaci sabbin daliban da a matsugunnin jami'ar na din-din da ke Samaru, Zaria, jihar Kaduna da su yi riko da dokokin jami'ar

- Garba ya shawarce su da su kauracewa satar amsar jarabawa, shiga kungiyoyin asiri, shaye shaye, saka kaya da ba su dace ba da sauransu

A ranar Juma'a, jami'ar Ahmadu Bello, Zaria ta rantsar da dalibai 13,000 bayan samun gurbin karatunsu a zangon shekarar 2018/2019. Shugaban jami'ar, Farfesa Ibrahim Garba ya bukaci sabbin daliban da a matsugunnin jami'ar na din-din da ke Samaru, Zaria, jihar Kaduna da su yi riko da dokokin jami'ar.

Garba ya ce ya zama wajibi dalibai su rinka kallon kawunasu a matsayin masu sa'ar samun gurbin karatu a jami'ar saboda a cikin dalibai sama da 40,000 da suka bayyana bukatar shiga makarantar, dalibai 13,000 ne kadai suka samu gurbi.

"Da wannan na ke so ku gane cewa samun gurbin karatunku a nan wata alfarma ce. Bukin antsuwar da kukai ta fara karatu a jami'ar a yau Juma'a, bukine da ya alamta cewa daga yau kun zama iyalan wannan jami'a."

KARANTA WANNAN: Harin da aka kai masallacin New Zealand: Abubuwan da muka sani zuwa yanzu

Gishirin zaman duniya: Jami'ar ABU Zaria ta yaye dalibai sama da 13,000
Gishirin zaman duniya: Jami'ar ABU Zaria ta yaye dalibai sama da 13,000
Asali: Depositphotos

Garba ya shawarce su da su tabbata sun kauracewa satar amsar jarabawa, shiga kungiyoyin asiri, shaye shaye, saka kaya da ba su dace ba da kuma kauracewa duk wasu munanan dabi'u.

Shugaban jami'ar sai kuma ya basu tabbacin cewa jami'ar na da kwararru kuma gogaggun lamai da ma'aikatan da za su tabbata sun taimaka masu wajen cimma bukatunsu na rayuwa.

"Jami'ar Ahmadu Bello jami'a ce da ke dauke da jinsuna daban-daban, al'adu da kuma addinai maban-banta. Ta na daya daga cikin manyan jami'i'o a Nigeria," cewar Garba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel