PDP ta dage sai ta lalata demokradiyarmu a Najeriya - Fadar Shugaban kasa

PDP ta dage sai ta lalata demokradiyarmu a Najeriya - Fadar Shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta soki jam'iyyar PDP a kan abinda ta kira yunkurin lalata demokradiyar Najeriya

- Fadar shugaban kasar ta ce jam'iyyar na PDP ta fara aikata wannan abin takaicin ne tun bayan da ta sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu

- Jam'iyyar adawar itama ta zargi jam'iyyar APC mai mulki da shirya magudin zabe a zabukan da za a maimaita a wasu jihohi

A daren ranar Alhamis 14 ga watan Maris ne fadar shugaban kasa da soki babban jam'iyyar adawa na Peoples Democratic Party PDP inda ta ce jam'iyyar tana iya kokarinta domin ganin ta lalata demokradiyar Najeriya tun bayan da ta sha kaye a zabe.

Wannan jawabin na fadar shugaban kasa yana zuwa ne a lokacin da jam'iyyar PDP ke zargin APC da shirin tayar da hankula a jihar Taraba saboda a zartar da dokan ta baci kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

PDP ta dage sai ta lalata demokradiyarmu a Najeriya - Fadar Shugaban kasa
PDP ta dage sai ta lalata demokradiyarmu a Najeriya - Fadar Shugaban kasa
Asali: Twitter

PDP kuma ta yi ikirarin cewa jam'iyya mai mulki na APC tana shirin tafka magudi a zaben jihar Sokoto ta hanyar amfani da sojoji domin razana masu zabe.

A yayin da ya ke mayar a martani a kan zargin, hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya ce radadin shan kaye ne yasa PDP ta ke furta irin wannan zancen.

Kalamansa: "Bana tunanin zamu ce komi a kan wannan zancen saboda sun sha kaye mafi girma a tarihin demokradiyar karni na 4. Jam'iyyar PDP tana aikata duk mai yiwuwa domin lalata demokradiyar kasarmu.

Idan ba su ne ke kan karagan mulki ba a jihohi ko shugabancin kasa, za suyi amfani da kowace hanya domin kawo cikas. Sai dai Shugaba Buhari ya gagare su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel