Rugujewar ginin Legas: Wata mata ta kashe kanta bayan mutuwar yaranta 2

Rugujewar ginin Legas: Wata mata ta kashe kanta bayan mutuwar yaranta 2

- Wata mata ta kashe kanta bayan da ta samu labarin cewa yaranta guda biyu na daga cikin wadanda suka mutu a cikin wani gini da ya ruguje a tsibirin Legas

- Rahotannin sun kara bayyana cewa matar haifi yaran guda biyu, wadanda ke da shekaru 6 da hudu, ta hanyar yi mata aiki

- Mazauna yankin da matar ta ke, sun labarta cewa ta sayi kwalbar maganin kwari mai suna 'Sniper'

Rahotanni sun bayyana cewa wata mata ta kashe kanta bayan da ta samu labarin cewa yaranta guda biyu na daga cikin wadanda suka muutu a cikin wani gini da ya ruguje a ranar Laraba a tsibirin Legas.

Rahotannin sun kara bayyana cewa matar haifi yaran guda biyu, wadanda ke da shekaru 6 da hudu, ta hanyar yi mata aiki. Matar da mijinta dai na zama ne a yankin Gambari da ke a tsibirin.

Mazauna yankin da matar ta ke, sun labarta cewa ta sayi kwalbar maganin kwari mai suna 'Sniper'.

KARANTA WANNAN: Zabi hudu: A yau INEC za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Rivers

Rugujewar ginin Legas: Wata mata ta kashe kanta bayan mutuwar yaranta 2
Rugujewar ginin Legas: Wata mata ta kashe kanta bayan mutuwar yaranta 2
Asali: Twitter

"Babu wanda ya san me za ta yi da wannan maganin kwari na 'Sniper'. Sai dai bayan 'yan mintuna, sai muka ga kwalbar maganin a kusa da inda ta ke kwance tana barci inda kuma muka gani ashe mutuwa ta yi," cewar wani makwabcin mamaciyar da ya bukaci a sakaya sunansa.

Jama'a da dama sun yi dafifi a gidansu domin jajantawa tare da yiwa mijinta da iyalanta ta'aziyya.

A wani labarin makamancin wannan kuwa, Yetunde, wacce yaronta ya samu mummunan hatsari, ta kadu matuka da ganin yaronta kwance cikin mawuyancin hali a asibiti, inda har ta kwashe sama da awanni 9 a sume ba tare da sanin inda take ba.

An hangota dai tana yawo a yankin babban asibitin tsibirin Legas inda ta ke ci gaba da neman magunguna da kuma abubuwan bukata da likitoci suka rubuta mata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel