Zabi hudu: A yau INEC za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Rivers

Zabi hudu: A yau INEC za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Rivers

- A yau ne ake sa ran jam'iyyun siyasa da suka da jam'iyyar PDP, AAC, APC da ma sauran jam'iyyu za su san makomarsu kan zaben gwamnan jihar Rivers da aka dakatar

- INEC ta kira wani taro na hukumar gudanarwarta domin karbar rahoton binciken da aka gudanar kan shiyyar Kudu maso Kudancin jihar

- A cewar wata majiyar, duk wani tsaiko da hukumar zata samu na daukar mataki guda daya kan zaben zai iya hadda rikicin siyasa a fadin jihar

Rahotanni sun bayyana cewa a yau ne ake sa ran jam'iyyun siyasa da suka da jam'iyyar PDP, AAC, APC da ma sauran jam'iyyu za su san makomarsu kan zaben gwamnan jihar Rivers da aka dakatar.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta kira wani taro na hukumar gudanarwarta domin karbar rahoton binciken da aka gudanar kan shiyyar Kudu maso Kudancin jihar.

Haka zalika hukumar zaben na iya karbar rahoto kan binciken da ta gudanar na dalilin tayar da tarzomar karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

KARANTA WANNAN: Harin da aka kai masallacin New Zealand: Abubuwan da muka sani zuwa yanzu

Zabi hudu: A yau INEC za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Rivers
Zabi hudu: A yau INEC za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Rivers
Asali: Twitter

Sai dai babban batun da ke kan gaba a hukumar INEC ya zuwa daren jiya shine dakatar da zaben jihar Rivers.

Wata majiya ta bayyana cewa, a yanzu hukumar INEC na da zabi hudu, inda za ta dauki zabi daya da zata yanke hukunci kan zaben jihar ta Rivers kamar yadda jaridar The Nation ta wallafo. Zabin hukumar sune:

  • Walau ta soke zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki na jihar Rivers kwata-kwata ko kuma ta ki soke zaben jihar.
  • Gudanar da zabe a gudumomi, rumfuna ko kuma yankunan da matsalolin zaben suka shafa.
  • Sanar da sakamakon zaben da hukumar ta tattara idan har sha'anin tsaro bai bada damar gudanar da sabon zabe ba.
  • Sanar da sakamakon zabe da kuma sanar da masu nasara da wadanda suka fadi kamar yadda yake a yanzu tare barin wadanda suka sha kasa garzayawa kotu

A cewar majiyar, duk wani tsaiko da hukumar zata samu na daukar mataki guda daya kan zaben zai iya hadda rikicin siyasa a fadin jihar

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel