INEC ta sanya ranar sake zaben Ebonyi

INEC ta sanya ranar sake zaben Ebonyi

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar Asabar, 23 ga watan Maris a matsayin ranar zabe zabe a jihar Ebonyi.

Za a sake zaben ne saakamakn rashin kammala zabe a wasu mazabu a zaben gwamna da na yan majalisar dokoki a jihar, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Andy Ezeani, sakataren INEC a Ebonyi, ya bayyana hakan a Abakaliki a ranar Juma’ a, 15 ga watan Maris, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto.

INEC ta sanya ranar sake zaben Ebonyi
INEC ta sanya ranar sake zaben Ebonyi
Asali: UGC

Ya lissafo wuraren da abun ya shafa kamar haka, Ezza ta arewa maso yamma; yankin Ekka dauke da mazabu 16 da kuma yankin Oriuzor dauke da mazabu 32.

Ezeani ya bayyana cewa za a sake zaben ne a mazabu 27 a yankin Okposi Umuoghara da ke Ezza ta arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Badakalar WAEC: Rayuwata na cikin hatsari - Wanda ke karar zababben gwamnan APC

A wani lamari na daban, mun ji cewa Dan takarar kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Nasarawa, David Ombugadu yayi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar.

INEC ta kaddamar dad an takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Sule, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

Amma da yake Magana da gidan talbijin din Channels Television a ranar Alhamis, 15 ga watan Maris, Ombugadu yayi zargin cewa anyi magudi a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel