Harin da aka kai masallacin New Zealand: Abubuwan da muka sani zuwa yanzu

Harin da aka kai masallacin New Zealand: Abubuwan da muka sani zuwa yanzu

- Wasu 'yan bindiga ya kashe akalla mutane 49 tare da jikkata 20 a yayim da suke gabatar da sallar Juma'a a wasu masallatai guda biyu da ke New Zealand

- Wannan ya zamo harin 'yan bindiga mafi muni a kasar da har Firam Ministan kasar, Jacinda Ardern ya bayyana harin a matsayin ta'addanci

- Kwamishinan 'yan sanda, Mike Bush ya ce an kashe mutane 49 a Masallatan guda biyu, yayin da ake tuhumar wani mutum mai shakaru 20 da laifin aikata kisan

Wasu 'yan bindiga ya kashe akalla mutane 49 tare da jikkata 20 a yayim da suke gabatar da sallar Juma'a a wasu masallatai guda biyu da ke New Zealand, wanda kuma ya zamo harin 'yan bindiga mafi muni a kasar da har Firam Ministan kasar, Jacinda Ardern ya bayyana harin a matsayin ta'addanci.

Wani dan bindiga da ya dauki bidiyon harin daga daya daga cikin masallatan da ke a birnin Christchurch ya kuma dora a shafin Facebook, ya haska yadda harin ya gudana, bayan wallafa wata sanarwa ta yin Allah wadai da bakin haure.

A halin yanzu dai New Zealand na fuskantar babbar barazanar tsaro a cewar Mr Ardern

KARANTA WANNAN: Badakalar WAEC: Rayuwata na cikin hatsari - Wanda ke karar zababben gwamnan APC

Harin da aka kai masallacin New Zealand: Abubuwan da muka sani zuwa yanzu
Harin da aka kai masallacin New Zealand: Abubuwan da muka sani zuwa yanzu
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu mutane hudu na garkame a hannun 'yan sanda bisa zarginsu da sa hannun a harin, wadanda dama tuni suna a kundin mutanen da rundunar ta sanyawa idanu.

Kwamishinan 'yan sanda, Mike Bush ya ce an kashe mutane 49 a Masallatan guda biyu, yayin da ake tuhumar wani mutum mai shakaru 20 da laifin aikata kisan.

Bidiyon kai harin da aka rinka yadawa a kafafen sadarwa na zamani, wanda dan bindigar ya dauka kuma ya haska shi kai tsaye, ya nuna shi a lokacin da ya ke tuka abun hawa zuwa daya daga cikin masallacin, inda ya shiga kai tsaye tare da harbin kan mai uwa da wabi.

Masu bautar, walau a mace ko a jikkace, na kwakkwance a kasa kamar yadda bidiyon ya nuna. Sai dai Reuters sun kasa gane sahihancin bidiyon.

Wani mutum ya ce ya na a masallacin Al-Noor, inda ya shaidawa manema labarai cewa dan bindigar fari ne, mai kaurin jiki kuma yana sanye da hular kwano da rigar kare shigar harsashe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel