Zaben Nasarawa: Dan takarar gwamna a PDP ya ki amincewa da sakamakon zabe, ya doshi kotu

Zaben Nasarawa: Dan takarar gwamna a PDP ya ki amincewa da sakamakon zabe, ya doshi kotu

- Dan takarar kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Nasarawa, David Ombugadu ya nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da aka yi

- David yayi zargin cewa anyi magudi kuma zai je kotu domin bi wa mutane hakkinsu

- INEC ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Sule, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar

Dan takarar kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Nasarawa, David Ombugadu yayi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar.

INEC ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Abdullahi Sule, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

Zaben Nasarawa: Dan takarar gwamna a PDP ya ki amincewa da sakamakon zabe, ya doshi kotu
Zaben Nasarawa: Dan takarar gwamna a PDP ya ki amincewa da sakamakon zabe, ya doshi kotu
Asali: Twitter

Amma da yake Magana da gidan talbijin din Channels Television a ranar Alhamis, 15 ga watan Maris, Ombugadu yayi zargin cewa anyi magudi a zaben.

Yayinda yake ganin laifin INEC da ta kaddamar da sakamakon,ya nuna karfin gwiwar cewa bangaren shari’a za ta taimaka masa wajen dawo da zabin mutane.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta fara rusa gine-ginen da aka yiwa alama bayan ruguzowar makaranta

Sai dai da yake mayar da martini ga zargin, zababben gwamnan jihar, Sule yace ya amince dari-bisa-dari dsa nasarar da yayi na lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel