Badakalar WAEC: Rayuwata na cikin hatsari - Wanda ke karar zababben gwamnan APC

Badakalar WAEC: Rayuwata na cikin hatsari - Wanda ke karar zababben gwamnan APC

- Abraham Adekunle, wanda ke kalubalantar sahihancin takardar jarabawar WAEC ta Abdulrazaq, ya koka kan cewar rayuwarsa na cikin hatsari

- Adekunle ya yi ikirarin cewa ya samu sakwannin kartakwana na barazana ga rayuwarsa daga shuwagabannin addinai dana al'umma

- Ya ce ya shigar da kara kotu akan kalubalantar sakamakon jarabawar WAEC ne saboda tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin yanzu ke yi

Abraham Adekunle, wanda ke kalubalantar sahihancin takardar jarabawar WAEC ta zababben gwamnan jihar Kwara karkashin jam'iyyar APC a zaben da ya gabata, Abdulrahman Abdulrazaq, ya koka kan cewar rayuwarsa na cikin hatsari.

Adekunle, wanda ya zanta da manema labarai a Ilorin a ranar Alhamis, ya yi ikirarin cewa wasu da bai san ko su waye ba suna kaiwa rayuwarsa farmaki.

Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsayin mai kishin kasa kuma wanda ya tabbatar da cewa babu wanda ya sanya shi kai zababben gwamnan kara kotu, ya yi ikirarin cewa ya samu sakwannin kartakwana na barazana ga rayuwarsa daga shuwagabannin addinai dana al'umma, inda kowa ke bukatarsa akan janye wannan karar da ya shigar kotu.

KARANTA WANNAN: Fashin bankin Offa: Mai shari'a ta dakatar da sauraron karar wadanda ake zargi saboda tsaro

Badakalar WAEC: Rayuwata na cikin hatsari - Wanda ke karar zababben gwamnan APC
Badakalar WAEC: Rayuwata na cikin hatsari - Wanda ke karar zababben gwamnan APC
Asali: UGC

Ya ce ya shigar da kara kotu akan badakalar sakamakon jarabawar WAEC din ne saboda tona asirin badakalar, da kuma tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin yanzu ke yi.

Ya bayyana cewa: "Mai makon a jinjina mani akan wannan kwarmaton, yanzu na zama tamkar saniyar ware a cikin al'ummata. Kuma ni banga wani dalili da zai sa a hantare ni ba saboda akwai ire iren wadannan badakalolin a fadin kasar, wadanda sam ba su dauki wani hankali ba.

"Kwarai ni dan jam'iyyar PDP, amma ba na yiwa jam'iyyata aiki ko wani aiki akan wannan lamarin, babu wanda ke daukar nauyi na. Ina kuma fatan samun kyakkyawan sakamakon akan wannan aiki nawa. Idan har muka ce muna yaki da cin hanci da rashawa kuma a hannu daya muna hantarar masu wannan yakin, to kuwa muna gini ne toka a ciki."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel