Fashin bankin Offa: Mai shari'a ta dakatar da sauraron karar wadanda ake zargi saboda tsaro

Fashin bankin Offa: Mai shari'a ta dakatar da sauraron karar wadanda ake zargi saboda tsaro

- Matsalar tsaro ta tilasta dage sauraron shari'ar mutane biyar da ake zarginsu da gudanar da fashi da makami a wani banki da ke Offa, jihar Kwara

- Mai shari'a Halimat Salman, wacce ta dage sauraron karar, ta ce ta yanke hukuncin daukar matakin ne saboda kiyaye lafiya da rayukan kowa da ke cikin kotun

- Mutane biyar da ake zargin sun hada da; Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salaudeen Azeez ana kuma Niyi Ogundiran

Rahotanni sun bayyana cewa matsalar tsaro ta tilasta alkalin babbar kotun jihar Kwara da ke da zama a Ilorin dage sauraron shari'ar mutane biyar da ake zarginsu da gudanar da fashi da makami a wani banki da ke Offa, jihar Kwara.

Wannan ya faru ne bayan da kotun ta fara sauraron karar da aka shigar, inda aka gabatar mata da wani da lamarin ya auku a gabansa, Hitila Hassan, karkashin jagorancin jami'i mai shigar da kara, Wahab Egbewole, kuma ya samu tantancewa daga lauyan wadanda ake kara, Mathias Emeribe.

Alkalin da ke sauraron karar, mai shari'a Halimat Salman, wacce ta dage sauraron karar, ta ce ta yanke hukuncin daukar matakin ne saboda kiyaye lafiya da rayukan kowa da ke cikin kotun.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kotu ta wanke lauyan tsohon gwamnan Osun da aka haramtawa aikin lauyanci

Hoto: Jerin wadanda ake zarginsu da kai harin fashi da makami a bankin Offa
Hoto: Jerin wadanda ake zarginsu da kai harin fashi da makami a bankin Offa
Asali: Depositphotos

Ta bayyana cewa: "Rahotannin da muka samu ba za su barmu mu ci gaba da sauraron karar a yau ba. Duk da cewa bani da wani aiki a gabana amma inaga zai fi kyau mu dage sauraron shari'ar har sai gobe.

"Saboda matsar tsaro da kuma kare rayukan wadanda ake tuhumar da ma na mutane da ke cikin kotun, dole na dage sauraron karar. Allah ya sa mu kai gobe cikin rai da lafiya domin ci gaba da shari'ar."

Mutane biyar da ake zarginsu wadanda a halin yanzu ke fuskantar tuhuma a kotun, bisa zarginsu da aikata fashi da makami a wani bankin Offa a ranar 5 ga watan Afrelu, 2018 sun hada da; Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salaudeen Azeez ana kuma Niyi Ogundiran.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel