Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Benue ta lissafa Sanata Dino Melaye da Gwamna Samuel Ortom cikin wadanda za suyi aiki a matsayin wakilan jam'iyyar a zaben gwamna na jihar za a maimaita

- Jam'iyyar ta kuma nada tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da tsohon gwamnan jihar, Gabriel Suswan da tsohon Ministan cikin gida, Abba Moro a matsayin wakilan zaben

- An mika sunayensu cikin jerin sunayen wakilai 24 da PDP ta mika a ofishin INEC na garin Makurdi a matsayin wakilansu na zaben

An nada Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita
An nada Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita
Asali: UGC

Jam'iyyar PDP a jihar Benue ta nada Sanata Dino Melaye da Gwamna Samuel Ortom a matsayin wakilan zabe da za suyi aiki a zaben gwamna da za a maimaita a jihar.

DUBA WANNAN: Zargin sayen kuri'a: Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin fitar da miliyan 233

Kazalika, jam'iyyar ta kuma zabi tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da tsohon gwamnan jihar, Gabriel Suswan da tsohon Ministan cikin gida, Abba Moro a matsayin wakilan zaben da za a gudanar ranar 23 ga watan Maris kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Jaridar ta ruwaito cewa an mika sunayensu cikin jerin sunayen wakilai 24 da PDP ta mika a ofishin Hukumar Zabe mai zaman Kanta INEC na garin Makurdi a matsayin wakilansu na zaben.

Hukumar ta INEC ta kuma ce babu wata kotu da ke da ikon hana ta maimaita zabe a jihar Adamawa a wasu wuraren da zaben bai kammala ba da za a gudanar a ranar 23 ga watan Maris.

Kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Barrister Kassim Gaidam ya ce doka ba ta baiwa kotu ikon hana INEC gudanar da ayyukan ta ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel