Yanzu-yanzu: Gwamnatin Legas za ta fara rushe tsaffin gine-gine

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Legas za ta fara rushe tsaffin gine-gine

- Gwamna Ambode na jihar Legas ya lashi takobin rushe dukkan gine-ginen makarantu da ke unguwar Faji na jihar Legas

- Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne bayan rushewa da wani gini ya yi a unguwar

- Ambode ya yi korafin cewa duk da gargadin da aka yiwa masu gidaje da dama a unguwar, sun ki tashi daga gidajen domin a rushe su

Bayan rushewar da ginin wani makaranta da ke unguwar Faji na jihar Legas ya yi a jiya, Gwamna Akinwunmbi Ambide na jihar ya dau alwashin rushe dukan gine-ginen makarantun da akayi ba bisa ka'ida ba.

Channels TV ta ruwaito cewa Ambode ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba 13 ga watan Maris yayin da ya ke mayar da martani a kan damuwar da wasu mazauna unguwar suka nuna a kan makarantun da aka gina ba bisa ka'ida ba.

DUBA WANNAN: Zaben da za a sake a Kano na 'ko a mutu-ko a yi rai' ne: An bukaci a kama shugaban APC

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Legas za ta fara rushe tsaffin gine-gine
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Legas za ta fara rushe tsaffin gine-gine
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta ruwaito cewa ginin makarantar ya rubzo wa dalibai ne misalin karfe 9.45 na safiyar ranar 13 ga watan Maris inda daruruwan mutane da ke sama da kasan ginin suka makale a ciki na tsawon sa'o'i masu yawa har wasu ma sun rasu.

A kalla mutane 20 ne jami'an bayar da agajin gaggawa da al'ummar unguwar suka ceto daga rushashen ginin.

Gwamnan Ambode ya koka kan yadda masu gidaje a unguwar ba su bin kai'ida su fice daga gidajensu idan hukuma ta saka alaman rushe gidajen.

Ya ce: "A halin yanzu an sanar da ni cewa an ceto a kalla mutane 25 amma wasu sun mutu amma an sanar da mu cewar ginin ainihi ba makaranta bane. Ginin gida ne da aka kafa makaranta ba bisa ka'ida ba a hawa na biyu na benen.

"Kamar yadda muka fadi, muna gwaje-gwajen gini a unguwar nan kuma an gano wasu da ya dace a rushe su sai dai masu gidajen ba su son su fice amma dole za mucigaba da aikin rushewar domin kare rayyuka da dukiyoyin al'umma. Za mu rushe duk wani gini da gwajin ya nuna da dace a rushe shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel