Da duminsa: Kotu ta wanke lauyan tsohon gwamnan Osun da aka haramtawa aikin lauyanci

Da duminsa: Kotu ta wanke lauyan tsohon gwamnan Osun da aka haramtawa aikin lauyanci

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa wata kotun koli ta warware hukuncin da kwamitin ladaftar da masu aikin shari'a (LPDC) ya yanke a ranar 21 ga watan Mayu 2015, wanda ya haramtawa Kule Kalejaye (SAN) aikin lauyanci saboda karya dokar aiki.

Kwamitin LPDC ta kama Kalejaye wanda ya taba kasancewa lauyan jam'iyyar PDP da kuma gwamnan jihar Osun na wancan lokaci, Olagunsoye Oyinlola, da laifin tuntubar shugaban kwamitin kotun karbar korafe korafen zaben gwamnoni na jihar Osun a shekarar 2008, mai shari'a Thomas Naron, wanda shi Kalejaye ya daukaka kara kan wannan zargi da ake yi masa.

A hukuncin da suka yanke a ranar Juma'a, wani kwamitin mutane biyar da kotun koli ta kafa, ya yanke hukuncin amincewa da daukaka karar Kalejaye, la'akari da cewar kwamitin LDPC ba shi da wata kwakkwarar hujja.

KARANTA WANNAN: Muna hasashen kawo karshen cutar kanjamau a Nigeria - Shugaba Buhari

Da duminsa: Kotu ta wanke lauyan tsohon gwamnan Osun da aka haramtawa aikin lauyanci
Da duminsa: Kotu ta wanke lauyan tsohon gwamnan Osun da aka haramtawa aikin lauyanci
Asali: UGC

Mai shari'a Centus Nweze ne ya karanta hukuncin kotun kolin inda aka wanke Kalejaye daga zargin da ake yi masa, da kuma kawo karshen haramtawar da aka yi masa na aikin lauyanci.

Cikakken labarin yana zuwa...

A wani labarin kuma; Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rahoton safiyon da aka gudanar kan cutar nan da ke karya garkuwar dan Adam da aka fi saninta da Kanjamau [NAIIS], yana mai cewa akwai hasashen kawo karshen cutar a Nigeria.

Da ya ke kaddamar da rahoton safiyon NAIIS a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaba Buhari ya ce akwai ingantattun alkaluma da aka amince da su dangane da cutar ta kanjamau da zai yi kyakkyawan tsari a Nigeria na kawo karshen yaduwar cutar mai karya garkuwar dan Adam da kuma kare kasar daga shigowar cutar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel