Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta fara rusa gine-ginen da aka yiwa alama bayan ruguzowar makaranta

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Lagas ta fara rusa gine-ginen da aka yiwa alama bayan ruguzowar makaranta

Gwamnatin jihar Lagas ta fara rushe gine-ginen da aka yi wa alamu a unguwar Freeman a yankin Faji da ke birnin Lagas, inda wani gini ya rushe a ranar Laraba, 13 ga watan Maris.

Daga cikin wadanda rushewar ginin ya cika dasu harda yara kanana, wadanda makarantarsu ke a saman benen day a rushe.

Hakan na zuwa ne bayan Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Lagas, Akinwunmbi Ambodeya dau alwashin rushe dukan gine-ginen makarantun da akayi ba bisa ka'ida ba.

Channels TV ta ruwaito cewa Ambode ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba 13 ga watan Maris yayin da ya ke mayar da martani a kan damuwar da wasu mazauna unguwar suka nuna a kan makarantun da aka gina ba bisa ka'ida ba.

Ginin makarantar ya rubzo wa dalibai ne misalin karfe 9.45 na safiyar ranar 13 ga watan Maris inda daruruwan mutane da ke sama da kasan ginin suka makale a ciki na tsawon sa'o'i masu yawa har wasu ma sun rasu. A kalla mutane 20 ne jami'an bayar da agajin gaggawa da al'ummar unguwar suka ceto daga rushashen ginin.

KU KARANTA KUMA: An haifi jaririya dauke da rubutun sunan Allah a Sokoto

Gwamnan Ambode ya koka kan yadda masu gidaje a unguwar ba su bin kai'ida su fice daga gidajensu idan hukuma ta saka alaman rushe gidajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel