Muna hasashen kawo karshen cutar kanjamau a Nigeria - Shugaba Buhari

Muna hasashen kawo karshen cutar kanjamau a Nigeria - Shugaba Buhari

- Buhari ya bayyana rahoton safiyon da aka gudanar kan cutar nan da ke karya garkuwar dan Adam da aka fi saninta da Kanjamau [NAIIS]

- Shugaban kasar ya ce akwai ingantattun alkaluma da aka amince da su dangane da cutar ta kanjamau da zai yi kyakkyawan tsari a Nigeria na kawo karshen yaduwar cutar

- Ya ce rahotanni sun bayyana cewa masu shekaru 15 zuwa 49 da ke dauke da cutar na da kashi 1.4. Kuma akwai kiyascin 'yan Nigeria 1.9m da ke rayuwa da cutar kanjamau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rahoton safiyon da aka gudanar kan cutar nan da ke karya garkuwar dan Adam da aka fi saninta da Kanjamau [NAIIS], yana mai cewa akwai hasashen kawo karshen cutar a Nigeria.

Da ya ke kaddamar da rahoton safiyon NAIIS a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaba Buhari ya ce akwai ingantattun alkaluma da aka amince da su dangane da cutar ta kanjamau da zai yi kyakkyawan tsari a Nigeria na kawo karshen yaduwar cutar mai karya garkuwar dan Adam da kuma kare kasar daga shigowar cutar.

"An gudanar da binciken safiyon NAIIS domin samun ingantattun alkaluman da muke bukata da zasu taimaka wajen kawo karshen cutar kanjamau a Nigeria.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: APGA ta garzaya kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben Zamfara

Muna hasashen kawo karshen cutar kanjamau a Nigeria - Shugaba Buhari
Muna hasashen kawo karshen cutar kanjamau a Nigeria - Shugaba Buhari
Asali: Facebook

"Bisa rahoton da muke da shi a yanzu, masu shekaru 15 zuwa 49 da ke dauke da cutar na da kashi 1.4. Akwai kiyascin cewa akalla 'yan Nigeria 1.9m ne ke rayuwa da cutar kanjamau, inda akalla miliyan daya ke karbar magani.

"Na ji dadin yadda rahoton ya bayyana cewa 'yan Nigeria kalilan ne ke dauke da wannan cuta ta kanjamau. Sai dai, ba zamu yi murnar wannan nasarar ba tun yanzu, ganin cewa kusa 'yan Nigeria miliyan daya ne ke rayuwa da cutar kuma ba sa karbar magani. Yanzu muna da alkaluman da za su taimaka wajen yaki da wannan cutar, da nufin kawo karshenta kafin shekarar 2030.

"Hakika wannan rana ta bayyana kyakkyawar makomar da Nigeria ke da shi na kawo karshen cutar kanjamau da ta kashe mata da mazan kasar nan. Tun yanzu muna ganin kawo karshen cutar zuwa 2030. Da wannan ya kamata mu yi aiki tukuru domin ganin mun cimma wannan muradin," a cewar shugaban kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel