An kulla mikirci domin karya ni a siyasance - Okorocha ya yi korafi

An kulla mikirci domin karya ni a siyasance - Okorocha ya yi korafi

Gwamnan jihar Imo Rochas Okoroha ya ce ya yi imanin cewa an hana shi shedar lashe zaben mazabar Imo ta Yamma ne saboda ana son ayi masa illa a siyasa gabanin shekarar 2023.

Ya kuma ce taron dangin da aka yiwa dan takarar gwamna na zaben ranar 9 ga watan Maris da ya fi so, Uche Nwosu na jam'iyyar Action Alliance (AA) yana daga cikin makircin da ake kullawa domin ganin bayansa.

Ya yi zargin cewa baturen zabe na jihar Imo ya aikata abinda masu gidansa suka fada masa ne kuma zalunci ne aka yi masa.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a masaukinsa na Asokoro da ke Abuja, Okorocha ya ce ya yi imanin cewa an hana shi shedar lashe zaben ne domin ba a son ya samu wata shugabanci a majalisar dattawa.

DUBA WANNAN: Zaben da za a sake a Kano na 'ko a mutu-ko a yi rai' ne: An bukaci a kama shugaban APC

An kulla mikircin karya ni a siyasance - Okorocha ya yi korafi
An kulla mikircin karya ni a siyasance - Okorocha ya yi korafi
Asali: UGC

A cewarsa, yana jiran Hukumar Zabe INEC tayi masa bayanin dalilin da yasa ba a gayyace wurin taron karbar takardan shedan lashe zabe na zababun sanatoci da 'yan majalisun dokokin tarayya ba.

Ya ce: "Doka ta tanadi cewa muddin an ambaci sunan mutum a matsayin wanda ya lashe zabe, ya zama dole a mika masa takardan shedan lashe zabe.

"Na san kowa ya lura ban hallarci taron karbar shedan lashe zaben ba. Hakan ya faru ne saboda INEC ta cire suna na daga jerin sunyaen sanatocin da aka zaba duk da cewa baturen zabe ya sanar da cewa ni na lashe zabe.

"Ina jiran a sanar da ni dalilin da yasa aka cire suna na. Wata kila suna wani shiri na musamman ne domin an sanar da ni cewa muddin INEC ta sanar mutum ya ci zabe ya zama dole a mika masa shedan lashe zaben.

"Naji jita-jitar cewa wai na tilastawa baturen zabe sanar da cewa na lashe zabe ne. Ni banda masaniya a kan hakan domin babu wani abu mai kama da haka da ya faru.

"Mene zai sanya ka tilastawa mutum fadin sakamakon zabe bayan kai ne ka lashe zaben? Ina son in sanar da duniya cewa wannan zargin ba gaskiya bane kawai dai akwai makircin da ake kulawa ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel