Da dumin sa: An tsinci gawar dan kasar wajen da aka sace a jihar Kano

Da dumin sa: An tsinci gawar dan kasar wajen da aka sace a jihar Kano

Labari da dumi-dumin sa da muka samu da majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa an tsinci gawar dan kasar Lebanon din nan da wasu 'yan bindiga suka sace yana kan aikin sa a jihar Kano ranar Talatar da ta gabata da sanyin safiya.

Sai kuma kimanin kwanaki uku da sace mutumin wanda bamu tabbatar da sunan sa ba, rahotanni sun zo na cewa an tsinci gawar sa a kan hanyar Maiduguri, duk dai a jihar ta Kano a ranar Alhamis.

Da dumin sa: An tsinci gawar dan kasar wajen da aka sace a jihar Kano
Da dumin sa: An tsinci gawar dan kasar wajen da aka sace a jihar Kano
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sarkin Kano ya jinjinawa Kwamishinan 'yan sanda CP Wakili

Kamar dai yadda mai karatu zai iya tunawa, mun kawo maku labarin cewa wasu mutane 4 ne da ba a san daga ina su ka fito ba, su ka sace wani kwararren bakanike (watau Injiniya) da ke aiki a Kano.

Wani mutumi da ya bada shaidar abin da ya faru, ya tabbatarwa ‘yan jarida cewa an harbe Direban motar da wannan kwararren bakanike yake ciki kafin a yi gaba da shi da kimanin karfe 7:40 na safiyar Ranar Talata.

‘Yan Sanda sun dai fitar da jawabi inda su kace babu shakka wannan abu ya faru, kuma tuni aka soma bincike domin gano bakin zaren. Abdullahi Haruna, wanda ke magana a madadin ‘yan sandan Kano ya fadi wannan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel