Arewa za ta gabatar da dan takarar shugaban kasa da yafi cancanta a 2023 - Shettima

Arewa za ta gabatar da dan takarar shugaban kasa da yafi cancanta a 2023 - Shettima

- Shugaban kungiyar matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, ya bayyana gwamnatin Buhari a matsayin gwamnatin da ta gaza

- Yerima Shettima ya bayyana cewa Arewa ta shirya gabatar da wani mutum nagari da zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023

- Ya kuma ce yana goyon bayan matakin da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya dauka na garzayawa kotu kan zaben 2019

Shugaban kungiyar matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, ya bayyana gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin da ta gaza tare da bayyana cewa Arewa ta shirya gabatar da wani mutum nagari da zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023.

A cikin zantawarsa da manema Labarai, Shettima ya bayyana cewa da yawan 'yan Nigeria sun dauka cewa APC za ta gudanar da sahihin zabe kamar yadda PDP ta yi a baya, "amma yadda jami'an tsaro suka ci karensu ba babbaka a zaben ya bamu kunya, mun karaya da shugabancin APC."

"Idan har aka yi nazari, za a gane cewa banbancin kuri'un da ke tsakanin PDP da APC a Arewa, a lokacin zaben shugaban kasa, ya sha banban sosai da kuri'un da aka gani a zaben gwamnoni, wannan ne ya sa jama'a suka fara zargin cewa an tafka uban magudi," cewar shettima.

KARANTA WANNAN: Assha: Dan daba ya kashe wanda ake zargi da kashe wata mata tare da kona gawarsa

Arewa za ta gabatar da dan takarar shugaban kasa da yafi cancanta a 2023 - Shettima
Arewa za ta gabatar da dan takarar shugaban kasa da yafi cancanta a 2023 - Shettima
Asali: Depositphotos

Yerima Shettima ya ce rikicin siyasa da ya mamaye jihohin Bauchi, Kano, Sokoto da sauransu, inda har al'umma ke zanga zanga saboda wasu marasa kishi suna son sauya ra'ayin jama'a, "Hakan kawai ya nuna cewa sakamakon zaben da ake so a kakaba ba shi ne zabin jama'a ba, kawai ana son a yi rashin adalci a lamarin."

"Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya garzaya kotu saboda yana ganin cewa an tafka magudi a zaben kuma yana da yakinin cewa za ayi masa adalci. Nima ina ganin cewa zuwan sa kotun shine matakin da ya dace."

Danagane da nade naden mukamai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a Arewacin Nigeria kan tsaro, Shettima ya ce: "Duk shuwagabannin tsaro da aka nada daga Arewa, an nada su ne saboda rikicin da ake yi a Arewa. Idan har Arewa ake magana, to wannan gwamnatin ta mayar da hankali akan shiyyar Kudu masu Yamma ne kawai wannan ma ya sa muka fara tunanin bayan mulkinsa, to Arewa za mu sake neman shugabancin kasar a 2023, don ba ayi mana adalci ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel