Kwankwaso yayi tsokaci game da maganar kin biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Kano

Kwankwaso yayi tsokaci game da maganar kin biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Kano

Jagoran darikar siyasa ta Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci game da maganar kora da kuma kin biyan mafi karancin albashin ma'aikatan jihar Kano da ake zargin dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP ta jihar, Abba K Yusuf zai yi idan ya lashe zabe.

Kwankwason dai ya karyata dukkan rahotannin da ke yawo akan batun inda ya kuma alakanta maganar da cewa, tsabar karairayi ne kawai irin na gwamnatin jihar mai ci yanzu marasa kan gado da nufin dusashe hasken tauraruwar su.

Kwankwaso yayi tsokaci game da maganar kin biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Kano
Kwankwaso yayi tsokaci game da maganar kin biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Kano
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin rumfunan da za'a sake zabe a jihar Kano

Sanata Kwankwaso ya bayyana a hakan ne a wata sanarwa da ya bayar ta hannun mai magana da yawunsa, Hajiya Binta Spikin a ranar Alhamis din da ta gabata.

A cikin sanarwar, Kwankwaso ya bayyana cewa labaran dake yawo a shafukan sadarwar zamani na cewa zai umarci dan takarar jam’iyyar PDP, Injiya Abba Kabir Yusuf, ya kori dukkan ma’aikatan da gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Injiniya Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC karya ne.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan gari a unguwar Itafaji dake a garin Legas mun samu labarin cewa sun yiwa gwamnan jihar Akinwunmi Ambode ruwan duwatsu yayin da yake barin wurin ginin makarantar nan da ya ruguje da daliban Firamare akalla 80.

Su dai mutanen garin wadanda ke cikin yanayi irin na kaduwa da bakin ciki, sun tattaru a wurin makarantar suna alhini tare da ayyukan ceto sauran yaran da ake tunanin buraguzan gini ya danne su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel