Zagaye na biyu: Ba zamu yi sakaci ayi mana sakiyar da ba ruwa ba - Osinbajo

Zagaye na biyu: Ba zamu yi sakaci ayi mana sakiyar da ba ruwa ba - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kada su huta ko su yi sakaci gabannin zaben gwamnoni da za a sake gudanarwa a ranar 23 ga watan Maris a wassu jihohi.

Mista Osinbajo ya fadi hakan ne yayinda yake jawabi ga masu biyayya ga jam’iyyar a liyafar cin abinci na kungiyar PMB/PYO Volunteers Appreciation a dakin taro dake fadar shugaban kasa a ranar Alhamis a Abuja.

Hukumar INEC ta kaddamar da 23 ga watan Maris a matsayin ranar sake gudanar da zabbuka a jihohin Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Plareau da Sokoto inda aka bayyana zabbuka a matsayin ba kammalalle ba.

Zagaye na biyu: Ba zamu yi sakaci ayi mana sakiyar da ba ruwa ba - Osinbajo
Zagaye na biyu: Ba zamu yi sakaci ayi mana sakiyar da ba ruwa ba - Osinbajo
Asali: Facebook

Ya gode wa mahalarta akan jajirci da yarda da suka nuna, inda yake cewa tare da sake zaban shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu, Najeriya ta kasance a tafarkin cigaba.

Mista Osinbajo ya mika jajen jam’iyyar APC ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su yayin gudanar da zabe.

Ya bayyana cewa yakin neman zaben ya kasance yunkurin mutanen Najeriya wadanda yace sun kasance tare da cikakkiyar yarda da goyon baya ga shuwagabannin su ba tare da mika bukatu masu yawa ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi

Mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta cimma nasarori da dama a cikin shekaru hudu, an cimma wannan nasaran ne saboda gaskiya da martabar shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel