Kungiyoyi sun bukaci EFCC da ta hukunta Ganduje kan zargin cire N235m don siyan kuri’u

Kungiyoyi sun bukaci EFCC da ta hukunta Ganduje kan zargin cire N235m don siyan kuri’u

Wasu kungiyoyin jama’a a jihar Kano sun yi kira ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da ta hukunta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan zargin cire naira miliyan N235.5 daga baitul malin gwamnatin jihar gabannin sake zaben da za a yin an da kwanaki tara.

A wani korafi da kungiyar ta aike ma EFCC mai sunan “Korafi akan gwamnatin jihar Kano kan yunkurin siyan kuri’u gabannin zaben gwamna da za a sake gudanarwa a ranar 23 ga watan Maris a Kano” dauke das a hannun Comrade Kabiru Saidu Dakata, da Comrade Abdulrazaq Alkai jagororin kungiyar, sun bukaci hukumar da ta binciki kudaden da aka cire.

Kungiyoyi sun bukaci EFCC da ta hukunta Ganduje kan zargin cire N235m don siyan kuri’u
Kungiyoyi sun bukaci EFCC da ta hukunta Ganduje kan zargin cire N235m don siyan kuri’u
Asali: Twitter

Masu karan sun bayyana cewa “Muna fatan jan hankalinku akan wani cire kudi mai cike da zargi N235,500,000 daga baitul malin gwamnatin jihar Kano ta ma’aikatar kananan hukumomi.”

Ta kuma ci gaba da zargin cewa, “An tura kudaden da aka cire ga kananan hukumomi daban-daban inda INEC ta shirya sake zabe a ranar 23 ga watan Maris a jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi

“Kungiyar na sane da kokarin hukumar na son hana duk wani siyan kuri’u, musamman ta hanyar karfafa wa yan Najeriya gwiwar kawo rahoton wani lamari na siyan kuri’u gar eta, imam ta hanyar lambobin wayar da ta saki ko kuma ta sauran hanyoyi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel