Ku gaggauta gyaran fasalin zabe da wuri – Shugaban INEC ga majalisar dattawa

Ku gaggauta gyaran fasalin zabe da wuri – Shugaban INEC ga majalisar dattawa

- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci zababbun ‘Yan majalisar dattawa da su yi gaggawan fara aiki a kan sabon tsarin zaben kasar

- Yakubu ya sanar musu cewa ba da dadewa ba INEC za ta fara hada nazarin da ta yi game da zaben 2019

- Yace ta hakan ne za a yi saurin fahimtar alkiblar da zaben 2023 zai fuskanta domin fara shiri tun da wuri

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga zababbun ‘Yan majalisar dattawa da su yi gaggawan fara aiki a kan sabon tsarin zabe a kasar , da zaran sun shiga majalisa nan da wata uku.

Yakubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris a yayinda ya ke mika wa zababben sanata satifiket na shaidar cin zabe.

Ku gaggauta gyaran fasalin zabe da wuri – Shugaban INEC ga majalisar dattawa
Ku gaggauta gyaran fasalin zabe da wuri – Shugaban INEC ga majalisar dattawa
Asali: Original

“Ina kira a gare ku da cewa da kun shiga majalisa, farkon abin da za ku yi shi ne zama domin yin aikin da ya kamata na kammala tsara fasalin zaben da a gudanar na 2023.”

Yakubu ya sanar musu cewa ba da dadewa ba INEC za ta fara hada nazarin da ta yi game da zaben 2019, ta yadda za a yi saurin fahimtar alkiblar da zaben 2023 zai fuskanta domin fara shiri tun da wuri.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi

Idan ba a manta ba, majalisa ta aika wa Shugaba Muhammadu Buhari kudirin gyaran dokar zabe, amma ya ki amincewa ya sa mata hannu, a bisa dalilin cewa ya kudirin ya je a makare, daidai lokacin da zaben 2019 ya gabato.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel