Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi

Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki ganin gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar da takwaransa na jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, a lokacin da suka ziyarci fadar Shugaban kasa a jiya Alhamis, 14 ga watan Maris.

Dukkanin shugabannin biyu na fuskantar gwagwarmar zabe kimanin kimanin mako guda kenan, biyo bayan kaddamar da sakamakon zaben gwamna na ranar 9 ga watan Maris da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana a matsayin ba kammalalle ba.

A ranar Talata, kwanaki uku bayan zabe, gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Kashim Shettima (Borno), Badaru Abubakar (Jigawa), Yahaya Bello (Kogi) da Atiku Bagudu (Kebbi), Nasir El-Rufai (Kaduna) da Kayode Fayemi (Ekiti) ma sun ziyarci Villa.

Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi
Buhari ya kauracewa ganawa da gwamnonin Adamawa da Bauchi
Asali: Depositphotos

Babu wani dalili da aka bayar kan ziyarar guda biyu.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Abubakar da Bindow sun iso Villa ne daban-daban sannan suka nemi ganin Buhari. Sai dai basu taki sa’a ba domin Shugaban kasar bai gan su ba. Daga ne sai suka yi ganawar sirri da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo. Bayan ganawar sun ki amsa tambayoyi daga manema labarai.

KU KARANTA KUMA: Sarakuna daga jihohin arewa uku sun ziyarci Buhari, sun nemi ya kirkiri jihar Borgu (Hoto)

Wasu masu lura na ganin taron a matsayin wani yunkuri daga gwamnonin domin nean alfarmar Shugaban kasar don kare jiharsu daga fadawa hannun jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel