Yan bindiga sun kashe Musulmai 40 yayin da suke sallar Juma’a a Masallatai 2

Yan bindiga sun kashe Musulmai 40 yayin da suke sallar Juma’a a Masallatai 2

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wasu gungun yan bindiga sun kai munana hari a wasu Masallatan Juma’a guda biyu dake birnin Christchurch na kasar New Zealand, a yankin nahiyar Turai, inda suke bude ma Musulmai wuta yayin da suke sallar Juma’a.

Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan farmaki ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1:45 na rana, daidai lokacin da Musulmai suke gudanar da Sallar Juma’a, harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wasu kuma suka jikkata.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Faruk Lawan ne ya keta sakamakon zaben gwamnan Kano – Inji Kwamishina

Yan bindiga sun kashe Musulmai 40 yayin da suke sallar Juma’a a Masallatai 2
Masallacin
Asali: UGC

Wani Masallaci daya sha da kyar daya bayyana sunansa a matsayin Muhammad ya bayyana cewa akalla Musulmai dari hudu ne suka taru don gudanar da Sallar Juma’a a lokacin da maharan suka kaddamar da hare haren.

“Ina cikin sallah sai kwatsam naji karar harbe harbe, mutane kuma suna kuwwa, nan da nan na yi kokarin kamo dan kanina, amma hakan bai yiwu ba, kawai sai na zura a guje ta kofar baya, a yanzu haka dan kanina na can a cikin Masallacin, sai dai bai ji ciwo ba, amma basu da abincin da zasu ci.” Inji shi.

Muhammed ya kara da cewa Yansanda ne suka garkame Masallacin don gudun wani ya sake shiga cikin Masallacin, tare da tsaron Masallatan, sai dai har zuwa da daddare basu sakesu ba, kuma babu alamar zasu sake anan kusa.

Shima shugaban kasar New Zealand, Jacinda Ardern ya jajanta ma Musulman kasar, inda ya tabbatar da mutuwar mutane Arba’in (40), tare da mutane ashirin (20) da suka jikkata, haka nan ya bayyana cewa Yansanda sun kama dan bindiga guda daya, kuma a cewarsa dan asalin kasar Australia ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel