Amfani da 'earpiece' kan iya janyo cutar daji - Masana Kimiya 250 daga kasahe 40 sun yi ittifaki

Amfani da 'earpiece' kan iya janyo cutar daji - Masana Kimiya 250 daga kasahe 40 sun yi ittifaki

Gamayyar masana 250 daga kasashe 40 sun bayyana ra'ayinsu kan hadarin yawaitan amfani da na'urar sauraron magana da waya wato 'earpiece'.

A wata wasikar korafi da suka rubuta zuwa kungiyar kiwon lafiyan duniya WHO da majalisar dinkin duniya UN, masana Kimiyan sunce yawon iskar bature wato 'microwave radiation' na da matukar hadari ga lafiyan dan Adam.

Sunce wadannan kayan wayewan na da alaka da juna kuma suna shiga kwakwalwa; hakan na iya jawo ciutar daji a kwakwalwa.

"Bamu fara bincike kan irin ciwon da zai jiwa kwakwalwa ba, ballanta dokokin haramtashi. Amma an tunanin abu mai kyau ne gareku".

"Tun da 'Bluetooth' bai da hadari da yawa, ya na iya bude sashen jinin kwakwalwa, wanda zai iya sababba sinadarai da dama fita daga kwakwalwan." Wani farfesan jami'ar California ya laburta.

KU KARANTA: Dakarun Soji sun kara samun nasara kan yan Boko Haram

Bincike da aka gudanar kan dabbobi ya nuna cewa yawon iskar baturen an da alaka da cutar daji. Kana hukumar bincike kan cutar daji ta duniya ta alanta cewa iskar bature na iya janyo cutar daji.

Idan muka dawo gida Najeriya, Wasu yan bindiga sun kai mumunan hari ofishin yan sanda dake jihar Edo inda suka hallaka babban jami'i DPO, DCO da wasu mutane biyu da ya hada da wata yar sanda mai juna biyu.

Majiya ta bayyana cewa yar sanda mai juna biyu bata dade da zuwa ofishin ba daga Benin, inda suka hallakata. Wannan mumunan hari ya faru ne ranar Asabar, 13 ga watan Maris a hedkwatan Afuze dake karamar hukumar Owan ta gabas, jihar Edo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel