Shugaba Buhari yayi ta'aziyya ga 'yan Najeriyar da ibtila'i ya afkamawa

Shugaba Buhari yayi ta'aziyya ga 'yan Najeriyar da ibtila'i ya afkamawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyar sa ga wadanda ibtila'in rushewar gini a jihar Legas da kuma hadarin tankar mai a jihar Anambara da gwamnatin jahohi, yana mai nuna alhinin sa da kaduwa.

Shugaban kasar dai ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sa na dandalin sadarwar zamani na Facebook da Tuwita da daren yau.

Shugaba Buhari yayi ta'aziyya ga 'yan Najeriyar da ibtila'i ya afkamawa
Shugaba Buhari yayi ta'aziyya ga 'yan Najeriyar da ibtila'i ya afkamawa
Asali: Facebook

Mai karatu dai zai iya tuna cewa wani gini a garin Legas ya rufta da daliban makarantar firamare yayin da kuma wani hatsarin tankar mai ya auku a garin Onicha.

A wani labarin kuma, masu aikin ba da agaji a Legas na ci gaba da ceto mutanen da ke karkashin baraguzan ginin da ya rushe a ranar Laraba a unguwar Ita-Faaji da ke yankin Island a birnin.

'Yan sanda sun shaida wa majiyar mu ta BBC Hausa cewa zuwa yanzu mutum 50 aka zakulo yayin da mutum 11 kuma suka mutu.

Gwamnatin Jihar Legas ta ce za a gudanar bincike bayan an kammala aikin ceto, kuma za a hukunta duk wanda aka kama da laifi.

Zai yi wahala a san takamaiman yawan mutanen da ke cikin ginin a lokacin da abun ya faru, saboda gini ne mai dauke da gidajen mutane da kuma makarantar da ke da dalibai kusan 100.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel