Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a Birnin Gwari

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a Birnin Gwari

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai kauyen Jan Ruwa dake karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

A sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna, DSP Yakubu, ya fitar a yau, Alhamis, y ace ‘yan bindigar sun saci shanu ma su yawa sun gudu da su bayan kasha mutanen.

A cewar Yakubu, “a ranar 12 ga watan Maris, 2019 da misalign karfe 11:45 na safe, mun samu labarin cewar wasu ‘yan bindiga sun shiga kauyen Jan Ruwa a karamar hukumar Birnin Gwari kuma sun sace shanu masu yawa.

“Yan kungiyar ‘yan bijilanti na kauyen sun hada kansu tare da bin ‘yan bindigar zuwa cikin surkukin daji.

“An dade ana musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan bijilanti wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan kungiyar bijilantin da dama.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a Birnin Gwari
Gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-rufa'i
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa bayan an tura jami’an ‘yan sanda da Karin wasu ‘yan kungiyar bijilanti ne aka gano gawarwakin ‘yan bijilanti din da aka kasha.

Ya bayyana cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman, ya yi alla-wadai da kai harin tare da daukan alkawarin kamo ‘yan bindingar tare da gurfanar da su domin a hukunta su a kan wannan ta’addanci da su ka aikata.

DUBA WANNAN: Tazarcen Buhari: FG ta kafa kwamitin rantsar da shugaban kasa

Sanna ya cigaba da cewa, kwamishinan ya mika sakon ta’aziyyar sa ga ‘yan uwa da iyalan wadanda aka kashe tare da sanar da su cewar tuni rundunar ‘yan sanda ta tura jami’ai na musamman domin ganin an kama ‘yan bindigar nan bada dadewa ba.

A karshe ya nemi jama’a da su taimaka wa jami’an ‘yan sanda da muhimman bayanai da zasu taimaka wajen samun damar kiyaye afkuwar aiyukan ta’addanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel