Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun kona ofishin INEC, sun kashe DPO, DCO da yar sanda mai juna biyu

Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun kona ofishin INEC, sun kashe DPO, DCO da yar sanda mai juna biyu

Wasu yan bindiga sun kai mumunan hari ofishin yan sanda dake jihar Edo inda suka hallaka babban jami'i DPO, DCO da wasu mutane biyu da ya hada da wata yar sanda mai juna biyu..

Majiya ta bayyana cewa yar sanda mai juna biyu bata dade da zuwa ofishin ba daga Benin, inda suka hallakata.

Wannan mumunan hari ya faru ne ranar Asabar, 13 ga watan Maris a hedkwatan Afuze dake karamar hukumar Owan ta gabas, jihar Edo.

A bangare guda, yan bindigan sun kai hari ofishin hukumar gudanar da zab ta kasa mai zaman kanta wato INEC inda suka lalata kayayyakin zabe kuma suka kone motar yan sanda kirar Hilux kurmus.

Sunayen jami'an yan sandan da suka rasa rayukansu sune Mr. Tosimani Ojo, (DPO). Sajen Justina Aghomon (Mai juna biyun), Infekto Sado Isaac da Kofura Glory David.

KU KARANTA: Dakarun Soji sun kara samun nasara kan yan Boko Haram

Wani idon shaida, Mr Godwin Ikpekhia, ya bayyana cewa abun ya faru ne misalin karfe 8 na daren ranar Talata yayinda da dama ccikin yan sandan sun fita tare hanya.

Yace: "Kawai harbe-harbe muka far ji kuma babu wanda ya san abinda ya faru sai safiyar Laraba. shugaban yan sandan ofishin da wasu yan sanda uku aka kashe cikin ofishin."

"Yan bindigan basu tsaya a nan ba, sun karasa ofishin hukumar INEc inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi domin tsorata jami'an tsaron da ke wajen."

Kwamishanan yan sandan jihar, Mr. Muhammed Danmallam, wand aya ziyarci wajen tare da gwamnan jihar, Godwin Obaseki, sun jaddada cewa za'a kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel