Obasanjo da Atiku sun gana a Abeokuta

Obasanjo da Atiku sun gana a Abeokuta

- Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya gana da tsohon ubangidansa, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta

- Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya kuma sauke faralin sallarsa a masallacin da ked akin karatun Obasanjo

- An kuma tattaro cewa dan takarar Shugaban kasar ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban kasar

Rahotanni sun kawo cewa Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya gana da tsohon ubangidansa, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Atiku yayi ganawar sirri a cikin dakin karatun Olusegun Obasanjo da misalin karfe 1pm.

Obasanjo da Atiku sun gana a Abeokuta
Obasanjo da Atiku sun gana a Abeokuta
Asali: Facebook

An tattaro cewa tsohon mataimakin Shugaban kasa ya kuma sauke faralin sallarsa a masallacin sannan kuma ya ci abincin rana da Obasanjo kafin ya bar garin cikin sirri.

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: PDP ta zargi gwamnatin tarayya da shirin lashe Sokoto ta karfi da yaji

Rahoton yace babu wani cikakken bayani kan abubuwan da Atiku ya tattauna da tsohon Shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel